Masana kimiya na nazari kan sabon maganin sanko

SAnko

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Masana sun ce zubewar gashi abu ne da ke faruwa kulum

An gano cewa maganin da ake bai wa masu ciwon kashi da ake kira osteoprosis zai iya samar da waraka ga masu sanko.

Masu binciken sun ce sun gano cewa maganin yana tasiri a ramin gashi a gwajin da suka yi, inda yake sa gashi ya tsiro.

Yana kunshe da wani sinadari da ke dakile tasirin sindarin Protein da ke sa gashi ya zube da haifar da sanko.

Jagoran ma su binciken Dakta Nathan Hawkshaw ya shaidawa BBC cewa za a yi gwaji domin a tabbatar da maganin ba shi da illa ga mutane.

A yanzu magunguna biyu ne kawai ake da su na masu sanko:

  • Maganin minoxidil, na mata da maza.
  • maganin finasteride, na maza kawai.

Sai dai dukkaninsu na yin illa a jikin bil'adama, shi ya sa a mafi yawan lokuta masu sanko ke zuwa asibiti domin yi mu su dashen gashi.

Binciken da aka wallafa a Mujjalar PLOS Biology an yi shi ne a cikin wani dakin gwaji inda aka yi amfani da samfuri da ke dauke da gashin wasu maza su fiye da arba'in wadanda aka yi wa dashen gashi.

Masu binciken daga jami'ar Manchester, sun fara aiki ne kan wani sindari da ake kira cyclosporine A, wanda aka yi da shi tun daga shekarun 1980 a kan marasa lafiya da aka yi wa dashen koda ko hanta da saraunsu.

Masana kimiyar sun gano cewa maganin na rage tasirin sinadarin protein da ake kira SFRP1, wanda yake da muhimmanci wajan ragewa da kara tsawon gashi.

Sai dai saboda illar CsA ba za a iya amfani da shi ba akan ma su sanko.

Masu binciken sun sake yin nazari kan wani sinadari da ake kira WAY-316606 kuma sun gno cewa yana tasiri sosai wajan rage kaifin sinadarin protein.

Dakta Hawkshaw ya ce maganin zai iya sauya rayuwar mutane "ma su sanko" .

Shin meyake janyo sanko?

Zubewar gashi abu ne da ke faruwa a kowace rana wanda ba wani abin tashin hankali ba ne.

Wasu zubewar gashinsu na takaittacen lokaci ne yayin da na wasu na din-din ne.

Ya kamata ka ga likita:

  • Idan ka wayi-gari ka ga gashin ka ya zube
  • Idan kana da sanko a wasu sassa
  • Idan gashi mai yawa sosai ne ya zube
  • Idan kai na kaikaiyi da kuma zafi
  • Idan zubewar gashi na janyo damuwa

Kakakin kungiyar likitocin fata ta Birtaniya ya shidawa BBC cewa: "wannan bincike ne mai dadin ji."

"Masu binciken sun ce, zubewar gashi abu ne da ke faruwa kulum amma kuma yana janyo damuwa kuma yakan sa mutum ya rika saurin karaya."

An ce akwai bukatar ganin cewa an gudanar da karin gwaji kafin a yi amfani da magani a kan mutane da gashinsu ya zube.

"Akan haka idan aka sami sabon magani, labari ne mai dadin ji, saboda zai ba mutane damar amfani da wasu magunguna da za su yi tasiri ." a cewar likitan.