Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mata 100: Wace ce Justice Zainab Bulkachuwa?
Justice Zainab Bulkachuwa na daga cikin wadanda suka yi sa'ar samun ilimi mai zurfi tun shekara 40 da suka gabata, kuma ta yi karatun shari'ar zamani ne a lokacin da ake ganin cewa irin wannan karatu 'haramun ne, kuma duk lauya dan wuta ne,' ba ma ga mata ba kawai har da mazan.