Yadda nake ilmantar da marayun Boko Haram – Zannah Mustapha
Malam Zannah shi ne wanda ya samar da daya daga cikin makarantun firamare kalilan da suka rage a birnin Maiduguri, inda ake fuskantar tashin hankalin Boko Haram a Najeriya.
Har ila yau, tsohon lauyan ya taba taimaka wajen sako 'yan matan chibok 82 da Boko Haram suka sace.
A wata makarantar addinin Musulunci mai suna Future Prowess, malaman da suke koyarwar suna karantar da daliban kyauta, su ba su abinci da kayan makaranta da magani duka kyauta.
Hakan ya taimaka masa wajen lashe lambar yabo ta Hukumar Kula da 'Yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a bana.
A ranar Litinin ne za a karrama Malam Mustapha da lambar yabon a a bikin da za a yi a birnin Geneva na kasar Switzerland.