Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko sallar Juma'a ta wajaba ga wanda ya je Idi?
A yau Juma'a ce al'umar Musulmi a fadin duniya ke bikin sallar layya, wadda aka fi sani da babbar sallah.
Ana bukatar Musulmi ya sada zumunci da yawaita ayyukan neman lada a ranar.
Bayan saukowa daga sallar idi ake yanka dabbobi ga wadanda ke da hali.
Daga nan kuma sai maganar zuwa masallacin Juma'a. Ko mene ne bambancin yau da sauran ranakun Juma'a?
Ibrahim Isa ya tattauna da Sheikh Ibrahim Khalil, shugaban majalisar malamai ta jihar Kano a kan abubuwan da aka kwadaita wa Musulmi su yi a wannan rana da kuma batun ko sallar Juma'a ta wajaba a wannan rana: