Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ina so dana ya gaje ni a fim- Sadiq Sani Sadiq
Shahararren jarumin fina-finan Hausa na Kannywood a Najeriya, - Sadiq Sani Sadiq, ya ce yana so dansa ya gaje shi a duniyar fina-finai.
Sadiq ya shaida wa BBC Hausa hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da Nasidi Adamu Yahaya.
Jarumin ya kuma ce kwarewarsa ta iya taka ko wacce rawa ce ta sa ya lashe gasar jarumin jarumai sau uku a jere.