Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Da gaske Buhari yake yaki da cin hanci – Ribadu
Tsohon shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati, EFCC, Mallam Nuhu Ribadu, ya shaida wa BBC cewa da gaske gwamnatin Muhammadu Buhari take yi wurin yaki da cin hanci da rashawa.