Abu shida da za ku yi la'akari da su game da watan Ramadan

Dr Junaid Abubakar
Bayanan hoto, Dr Junaid Abubakar
Lokacin karatu: Minti 3

Watan Ramadana na shekarar 1447 bayan Hijira ya zo, inda Musulmai za su sauke ɗaya daga cikin ginshiƙan addininsu.

Musulmai a fadin duniya za su kwashe kwana 29 ko 30 suna ƙaurace wa ci da sha da saduwar aure da kuma duk wasu abubuwa da aka ayyana cewa za su iya karya masa azumi daga asuba zuwa faɗuwar rana.

A watan Ramadana ne aka fara saukar da Al-Qurani mai girma, kuma an ambaci azumin na Ramadana a ayoyi daban-daban a cikin littafin mai tsarki.

Dukkanin wanda ya cika sharuɗɗan da Musulunci ya gindaya, mace ko namiji, wajibi ne ya azumci watan, sai dai akwai waɗanda addini ya sassauta mawa.

Kasancewar Ramadana wata mai matuƙar tasiri a rayuwar Musulmi, shin wane shiri ya kamata mai tunkarar azumin ya yi?

BBC ta tuntuɓi Dr Junaid Abubakar, malamin addinin Musulunci a Najeriya:

1- Kyautata niyya

Dr Junaid ya bayyana cewa abu na farko da ya kamata Musulmi ya yi a lokacin da Ramadana ya tunkaro shi ne yin niyya tsarkakakka.

"Kyautata niyya ginshiƙi ne a addini baki ɗaya," a cewar Dr Junaid.

2- Sahihiyar tuba

Masallaci

Asalin hoton, Getty Images

Malamin ya ce abu na biyu da ya kamata mutum ya yi shi ne tuba daga zunubbai.

"Allah na son bayinsa ne shi ya sa ya sanya azumi ya zama farilla a gare su, kuma azmumi na taimakawa wajen hana mutum yin saɓon Allah," in ji Junaid.

Iadan muka lura, Allah ya ce a kame daga duk wasu abubuwa da ke ingiza mutum ya faɗa wa sabon Allah

"Saboda haka ɗaya daga cikin abubuwan da ya kamata mai azumi ya ƙuduri niyya a lokacin da azumi ya ƙarato shi ne tuba mai kyau, wato mutum ya ƙuduri aniyar ya yanke alaƙa da laifin da yake aikatawa, kuma ya yi niyyar cewa ba zai sake koma wa laifin ba har ƙarshen rayuwarsa badaina, sannan idan akwai haƙƙin wani da ka ci ko ka cutar da wani, ka ɗauki wannan abin ka mayar masa kuma ka nemi afuwarsa."

3- Sanin matsayin zamani da lokaci

Abu na uku da malamin ya ambata shi ne Musulmi ya san cewa a lokacin azmumi ne aka saukar da Al-Qurani, kuma a cikin watan ne aka keɓancewa daren lailatul Qadari.

"Kamar yadda ake ruɓanya lada ga wanda ya bi Allah, haka akan ruɓanya zunubi da mummunan sakamako ga wanda ya saɓa wa Allah," a cewar Dr Junaidu.

A cewar malamin yana da kyau mutum ya san matsayin wannan lokaci na Ramadan da kuma abin da ke tattare da shi.

4- Ƙaranta cin abinci

Malamin ya karanto wani hadisi, inda ya ce Manzon Allah ya ce: "babu wani abu da ɗan'adam yake ɗauke da shi na jakkar sharri kamar cikinsa, ya kamata ƴan lomomi kaɗan su ishi dan'adam domin ƙarfafa lafiyarsa."

Saboda haka Dr Junaid ya ce lokaci ne da ya kamata mutane, musamman masu yawan cin abinci su taƙaita irin abincin da suke ci.

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

5- Sanin maƙasudin azumi

Ya kamata mutum ya san mene ne hikima, ko kuma abin da azumi yake son cimmawa a jikin ɗan'adam.

"Abin da azumi ke son cimmawa a jikin ɗan'adam shi ne, yana son ya ɗauki mutum ya mayar da shi zuwa ga Allah, yana son ya mayar da shi mai tsantsar cin halas, yana son ya mayar da shi mai yawan son yin sadaka da kyauta," in ji Sheikh Junaid.

Ya bayyana cewa manzon Allah ya kasance ya fi yawan kyauta a lokacin azumin Ramadana kuma ya fi yawan karatun Qur'ani a cikin watan.

6- Saba wa rai da aikin alheri

Malamin ya bayyana cewa azumi lokaci ne da ya kamata mutum ya saba wa ransa da ayyukan alheri.

"Rai horonsa ake yi kuma rainonsa ake," a cewar Mallam.

"Kowane rai yana da ciwo, amma hanyar warkar da shi, ita ce saba masa da ayyukan alheri