Ra'ayi Riga: Kan ƙaruwar ƙwacen waya a arewacin Najeriya

Ra'ayi Riga: Kan ƙaruwar ƙwacen waya a arewacin Najeriya

Ƙwacen waya, na ci gaba da zama babbar matsalar tsaro a birane da dama na arewacin Nijeriya.

Ƴan daba na tare mutane a kan titi, wasu ma da rana tsaka suna yi musu barazana da wuƙaƙe, kafin raba su da wayoyinsu.

Har ta kai matasan na caka wuƙa, ko yankar mutum, abin da yakan zo da ƙarar kwana da jin raunuka a wasu lokuta.

Ta sai dai hukumomi na ɗaukar matakan da ba a saba gani ba ciki har da taƙaita zirga-zirgar babura da daddare a jihohi kamar Gombe da Neja da kuma Kano, don taƙaita aika-aikar masu ƙwacen waya.

To shin ko yaya girman wannan matsala ta ƙwacen waya?

Me ya janyo ƙaruwar wannan aika-aika a biranen arewacin Nijeriya?

Kuma me ya kamata a yi don magance matsalar?

Waɗannan na daga cikin batutuwan da shirinmu na ra'ayi riga na wannan makon ya tattauna a kai.