Abin da ya kamata ku yi idan maciji ya sare ku

Maciji ya sari wani mutum a hannunsa

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Labarin mutuwar wata matashiya, mai suna Ifunanya Nwangene, sakamakon saran maciji na ci gaba da ɗaukar hankalin ƴan Najeriya musamman a shafukan sada zumunta.

An tsinci gawar matashiyar mawaƙiyar a Abuja bayan da aka bayar da rahoton cewa maciji ne ya sare ta.

Rahotonni sun ce matashiyar mai shekara 26 ta rasu ne bayan kai ta asibitoci biyu a Abuja ba tare da samun maganin dafin maciji ba.

Lamarin ya ɗauki hankalin ƴan ƙasar da dama, musamman labarin rashin maganin dafin maciji a asibiti har biyu kuma a Abuja, babban birnin Najeriya.

Kodayake ɗaya daga cikin asibitocin ya musanta iƙirarin rashin maganin dafin, mutane na ci gaba da bayyana damuwarsu kan hatsarin saran maciji.

Kan haka ne BBC ta tuntuɓi likita don sanin matakan farko da suka kamata mutane su ɗauka da zarar maciji ya sare su.

'Matakan gaggawa da za ku ɗauka'

Dokta Nicolas Amani Hamman, babban jami'in asibitin kula da saran macizai na Kaltingo a jihar Gombe ya lissafa wasu muhimman matakan gaggawa da ya kamata mutum ya ɗauka kamar haka:

  • A yi gaggawar ɗaukar mutum daga wurin ko a kawar da macijin daga wurin
  • Mutum ya kwantar da hankali kar ya razana
  • A ba shi maganin rage raɗaɗi kamar Paracetamol
  • Kada ya yi amfani da gaɓar da aka sare shi, (Idan ƙafa ce kada ya taka)
  • Kada a ɗaure wurin da tsumma ko igiya (saboda idan an ɗaure ana tara gubar a wuri guda, lamarin da zai sa ta yi mummunan ɓarna, sannan jini zai daina gudana)
  • Kada a tsotsi wurin ko a yanki wurin da reza
  • Yi ƙoƙarin fahimtar nau'in macijin (girma da kalarsa), hakan zai taimaka wajen sanin maganin da za a ba ka a asibiti.
  • Kada a shafa komai a kan ciwon kafin zuwa asibiti
  • Cire abun hannu (Awarwaro da agogo, ko zobe) a hannun da maciji ya yi sara.
  • A guji amfani ko shan maganin gargajiya
  • A yi gaggawar zuwa asibiti.
Maciji na saran ɗan yatsar wani mutum

Asalin hoton, Getty Images

Me ya sa macizai ke sara?

Macizai kan yi sara ne tare da zuba dafi da nufin nakasa abin da suka sara.

Dokta Nicolas ya ce an halitta wa maciji dafi ne da nufin neman abinci da shi ta yadda zai zuba wa ƙananan halittun da zai yi kalaci da su idan ya gamu da su.

Mutane ba sa cikin abincin macizai, don haka suna sarar mutane ne da nufin kare kansu.

Sukan sari mutane idan suka matse su, ko suka taka su ba tare da sani ba.

A wasu lokuta macizai kan sari mutum ba tare da zuba masa guba ba.

Alamomin sarar macizai

A wasu lokuta maciji kan sari mutum ba tare da ya sani ba, sai daga baya ya fahimci hakan.

Kana haka ne Dokta Nicolas ya bayyana wasu alamomin da mutum zai gani a jikinsa idan maciji ya sare shi.

  • Jin zafi/raɗaɗi a wurin da aka sare shi
  • Ganin kumburi a wurin
  • Ganin zubar jini a wurin
  • Ganin shatin haƙoran macijin a wurin da ak sare shi
  • Yin amai
  • Yawan jiri
  • A wasu lokutan mutum ba zai iya motsa gaɓar da aka sare shi ba

Yaya girman saran macizai a duniya?

Wani rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar a 2012 ya ce a kowace shekara akan samun ƙiyasin saran macizai miliyan 5.5 a faɗin duniya.

Lamarin da ke haifar da mutuwar mutum tsakanin 20,000 zuwa 125,000 a kowace shekarar.

Mafi yawan mace-macen sun fi faruwa ne a yankunan karkara, inda ake da ƙarancin asibitoci, a cewar WHO.