Kududdufin da ba ya cika kuma ba ya ƙafewa a Najeriya

Akwai rafuka da tafkuna da dama a duniya, kuma Najeriya ma na da irin nata, waɗanda wasun su ke da abubuwa na ban al'ajabi.
Kududdufin Ado Waye wani ƙaramin tafki ne wanda masu bincike suka ce bai taɓa cika ba, duk iyakar ruwan sama, kuma duk tsawon damin, haka nan kuma bai taɓa ƙafewa ba duk tsawon rani.
Wani jami'in ma'aikatar yawon shaƙatawa a ya yi wa BBC bayani kan abubuwan al'ajabi na kududdufin.
Mista Adams ya ce duk abin da aka jefa a cikin kududdufin ba za a iya ciro shi ba.
Tafkuna irin wannan guda biyu ne kacal a fadin duniya, kamar yadda ya bayyana.
Ɗayan da ake da shi shi ne wanda yake a Colorado na ƙasar Amurka, sai kuma Ado Awaye da ke jihar Oyo a Najeriya.
Wasu na ganin cewa ya kamata Najeriya ta ci gajiyar kududdufin.
Masu ruwa da tsaki a Najeriya na ganin cewa hukumomin ƙasar ba su cika bai wa ɓangaren yawon bude ido muhimmanci ba.











