Zafin wuta na janyo tsufan mata da wuri

Bayanan sautiLafiya Zinariya: Zafin wuta na janyo tsufan mata da wuri
Zafin wuta na janyo tsufan mata da wuri

Masu kwashe tsawon lokaci suna aiki da wuta mai zafi matuka kan fuskanci matsalar yamushewar fata, wanda hakan kan janyo tsufan wasu mata da wuri.

Tsananin zafin kuma kann shafi lafiyar kwakwalwa, lamarin da ke janyo matsalar damuwa da yawan fushi ga mace wanda ta kwashe shekaru tana sana’ar da ta shafi wuta.

Sai dai shan madara ba ya maganin zafin wuta, kamar yadda wasu suka dauka a al’adance.

Dr. Rukayya Muhammed Babandi ta ce babu wata hujja a likitance da ke gaskata haka.

Haka kuma kasancewa wuri mai hayaki da yawa ba tare da iska sosai ba yana da illoli ga masu aikin wuta.

Illolin da hayaki kan haddasa sun hada da tari, sauyi a launin idanu da yanar ido da kuma matsalolin hanyoyin numfashi da gurbatar jini da cutukan zuciya da sauransu.

Sai dai wasu hanyoyin da likita ta ce mata da duk masu amfani da wuta za su iya bi wajen rage zafi da kuma hayakinta sun hada da rage zama na tsawon lokaci a gaban wuta da yin girki a wurin da ake samun isasshiyar iska.