Wane ne ya fi jin raɗaɗin rabuwa a soyayya?

...

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 5

Ko da yake tambaya ce mai haifar da mabambantan ra'ayoyi, abu ɗaya da ya ke tabbace shi ne rabuwar soyayya na haifar da mummunan baƙin ciki da ka iya ɗaukar lokaci mai tsawo kafin a iya farfaɗowa daga gare shi.

Babu shakka soyayya aba ce mai matuƙar nauyi a zuciya, kuma har yanzu ana shan wahala wajen tantance ainahin ma'anarta.

Tana da daɗi, wanda ba ya misaltuwa, kuma tana tasiri a tsarin halitta da tunanin bil'adama. Ta wani fannin ana bayyana ta a matsayin abu mai sarƙaƙiya, wadda ta ƙunshi tsananin neman kusanci da kuma kasancewa tare na tsawon lokaci.

Shi ya sa waɗanda suka faɗa cikinta kan tsinci kansu cikin wani yanayi a duk lokacin da batun rabuwa ya taso.

Maryam Hassan Baba, kwararriya kan inganta zamantakewar iyali, kuma mai shafin The Northern Therapist, ta ce idan ana magana ta rabuwa tsakanin masoya, "ba za a iya cewa ga wanda ya fi shan wahala ba, saboda akwai bambanci a kan yadda kowa ke ɗaukar damuwar da ya faɗa ciki da kuma yadda suke amayar da ita."

Mene ne girman munin rasa masoyi?

Maryam Baba ta ce wani bincike ya nuna cewa "raɗaɗin rabuwa da masoyi kusan ɗaya ne da na ciwon bugun zuciya. Abu ne da zai sa masoyi ya rasa gane yanzu ko shi wane ne, tun da ƙila a baya kana kallon kanka a matsayin mallakin masoyinka, kin fara hangen yadda za ki yi rayuwa da masoyinki, saboda haka idan ku ka rabu da shi tamkar rasuwa ce aka yi miki, duk kuwa da cewa mutumin yana raye.

Yadda mace ke ji idan ta rabu da masoyinta

A ɗabi'ance, a cewar Maryam Baba, mata sun fi maza nuna damuwarsu a fili a lokacin da suka rabu da masoyinsu. Sannan ta ce wasu daga cikin abubuwan da kan zo a ran mace sun haɗa da:

Rashin madafa: ''A al'adance namiji ne ya ke zuwa ya ce yana son mace, idan daga baya zo ya ce ba ya son ta, ita mace za ta ji cewa an yi watsi da ita," a cewar Maryam.

Abin kunya da gazawa: Bayan jin cewa an yi watsi da ita, wani abu da ke faruwa da budurwar da ta rabu da saurayinta shi ne jin cewa ta yi wani abin kunya. "Saboda daman shi (saurayi) ya zo ya ce yana son ta yanzu kuma da kansa ya ce ba ya yi, to akwai wani irin kunya da za ta ji kamar akwai wata gazawace daga ɓangarenta.'' in ji ƙwararriyar. Ta ƙara da cewa za ta yi tunanin al'umma za su ɗora mata laifin gazawa saboda ta gaza riƙe saurayinta.

Kuka da koke: Maryam ta ce kasancewar mata suna da Rauni, a mafi yawan lokuta damuwar rabuwa da masoyi ya fi nunawa ɓaro-ɓaro a wurin mace. "Mace za ta faɗa kai-tsaye abin da ya faru ta ɓangarenta, za ta yi kuka kuma za ta faɗa wa kowa saboda ta amayar da baƙin cikin da ke damun ta," kamar yadda ta shaida wa BBC.

Maryam Hassan Baba

Asalin hoton, Maryam Hassan

Bayanan hoto, Maryam Hassan Baba ƙwararriya ce a ɓangaren zamantakewar iyali

Yadda namiji ke ji idan ya rabu da masoyiyarsa

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ƙwararriyar ta yi bayani cewa daga hulɗarta da wadanda suka rabu da masoyan da suka rabu, akwai ɓangarori da dama da ɗabi'ar saurayi ke bambanta da ta budurwa bayan rabuwa:

Rashin son nuna gazawa: Maryam ta ce a mafi yawan lokuta mazan da kan je wurinta domin neman shawara bayan rabuwa ba su fitowa kai-tsaye su amince cewa rabuwa da masoyiyarsu ne ya jefa su damuwa. "Yana ganin gazawa ce, zai iya alaƙanta damuwarsa ga wasu abubuwan daban saboda yana ganin idan ya amince cewa rabuwarsu ta haifar masa da damuwa, to hakan gazawa ce a ɓangaren shi."

Haɗiye takaici: Ƙwararriyar ta ce ba kamar mata ba, maza ba su da saurin furta damuwarsu. "Kafin ya fito ya faɗa zai ta jure kewar, za iyi ta fama da zaman kaɗaici, ba kamar mace ba. Zai ci gaba da aiki, da raha domin kada a gane, idan kuma abin ya dame shi sosai zai riƙa keɓe kansa duk domin kada a gane halin da yake ciki."

Tunanin abin da al'umma za ta ce: Al'umma na da ɗabi'ar cewa bai kamata namiji ya nuna damuwarsa ba, in ji Maryam, inda ta ce hakan kan sanya maza ba su son su faɗa wa wani damuwar da suka shiga domin gudun kada a ce suna da raki.

Dabarun shawo kan raɗaɗin rabuwa da masoyi

  • Amincewa cewar rayuwar da kike yi da masoyinki a baya ta zo ƙarshe: Hakan na bai wa mutum damar ci gaba da rayuwa kamar kowa. "Wannan zai sa ki daina ƙoƙarin neman mutumin da ya rabu da ke, domin idan kika neme shi, shi kuma ya guje miki, wannan zai riƙa fama raɗaɗin rabuwar," in ji Maryam."Ƙila kin saba duk lokacin da kika kira shi a waya zai ɗauka, amma yanzu za ki yi ta kira ba ya ɗauka, ko kuma ya yanke wayar, wannan zai kawo wulaƙanci da ƙasƙanci, hakan zai ƙara damuwar rabuwa da masoyi".
  • Yin abin da zai maye miki abin da kike yi da masoyinki a baya: "Wata ƙila duk lokacin da kika tashi bacci kuna yin waya da shi, to idan kun rabu abin da ya kamata ki yi shi ne ki samu wani abu da za ki yi wanda zai ɗauke miki hankali a daidai lokacin da kika saba yin waya da shi a baya," kamar yadda ƙwararriyar ta bayyana. Ta ce idan ba ki yin komai a wannan lokacin zai riƙa tuna miki abin da kuka saba yi da masoyin a baya a daidai lokacin. Ta bayar da shawarar a maye gurbin hakan da karatu ko wani aiki na daban.
  • Mayar da hankali a karan kanki: Ki yi ƙoƙarin gane abin da ke sanya ki raha ko ɗebe miki kewa, misali zama da iyaye ko ƙawaye, ko zuwa wurin motsa jiki ko kuma dai wata ɗabi'a ta daban.
  • Addua: Maryam ta ce addu'a na da matuƙar muhimmanci, duk da cewa wasu na ganin kamar rabuwa da masoyi bai isa ya zama abin da mutum za iyi addu'a a kai ba. "Yin addu'a na nufin cewa kin amince cewar abin da ya faru, ya faru, kin yarda cewa kin shiga wani hali na matsala, wannan zai sanya ki saki ranki har raunin ya warke cikin hanzari," in ji Maryam.