Fitattun ƴanƙwallon Afirka da ba za su je Gasar Kofin Duniya ta 2026 ba

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Ahmad Bawage
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 3
Yayin da gasar Cin Kofin Duniya ke ƙaratowa, ƙasashe da dama musamman waɗanda za su halarci gasar sun fara shirye-shiryen tafiya nan ba da jimawa ba.
A bana ƙasashe 48 ne za su je gasar, wadda Amurka da Canada da kuma Mexico za su karɓi bakunci.
A ɗaya gefe, yayin da waɗanda za su je gasar da kuma ƴan kwallonsu ke shiri, wasu ƙasashen a gida za su kalli gasar -saboda kasa samun damar halarta.
A wannan labari, mun yi duba kan fitattun ƴanƙwallon Afrika da ba za su je gasar ba.
Victor Osimhen - Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Victor Osimhen wanda ke taka leda a Galatasaray, ya zura kwallaye 33 a dukkan fafatawa da ya yi wa ƙungiyar a bana, inda suke kan hanyar lashe gasar Turkiyya.
Ɗan wasan gaban Najeriyar, na cikin jerin ƴan wasan da ba za su je gasar kofin duniya ba, saboda ƙasa samun gurbi da ƙasarsa ta yi - inda ta kare maki ɗaya kasan Afirka ta Kudu.
Najeriya ta yi rashin nasara a hannun Kongo a bugun fenariti wanda aka buga bayan sauya Osimhen, abin da ya sa ƙasar ta kasa zuwa gasar kofin duniya.
Serhou Guirassy - Guinea

Asalin hoton, Getty Images
Serhou Guirassy ya assasa kansa a matsayin ɗaya daga cikin ƴan wasan gaba mafi hazaka a duniyar kwallon kafa, inda ya zura kwallaye 62 a Bundesliga a cikin kakar wasanni uku da suka gabata, sannan babu ɗan wasan da ya ci kwallo sama da 13 wanda ya zura a gasar Champions League na kakar 2024-25.
Kuma shi ne na huɗu a yawan cin kwallaye a gasar Bundesliga a bana.
Sai dai, ba zai samu damar zuwa gasar kofin duniya ba saboda ƙasarsa ta Guinea ta fita tun a zagayen farko na neman gurbi a ɓangaren Afirka.
Inda suka kare a matsayi na huɗu a rukuninsu, nasara huɗu kacal da kuma canjaras guda uku a cikin wasanni goma.
Bryan Mbeumo

Asalin hoton, Getty Images
Bryan Mbeumo ɗan wasan gaban Manchester United na cikin sahun ƴan wasa da ba za su halarci gasar kofin duniya ba.
Hakan ya zo ne bayan gaza taimaka wa ƙasarsa ta Kamaru samun gurbin zuwa gasar.
Mbeumo ya zura wa Manchester United kwallaye takwas a gasar Premier a bana, inda suke matsayi na uku a teburi a koƙarinsu na zuwa gasar Champions League a baɗi.
Pierre-Emerick Aubameyang - Gabon

Asalin hoton, Getty Images
Pierre-Emerick Aubameyang na cikin zaratan ƴan wasa da ba za su je gasar kofin duniya ba , bayan da ƙasarsa ta ƙasa taɓuka abin kirki a wasannin neman gurbi.
Sun kare a matsayi na karshe a kasan rukunin F, inda ministan wasannin ƙasar na lokacin ya kwatanta hakan da "abin kunya".
Aubameyang ya zura kwallo ɗaya tal a gasar Afcon 2025 da aka yi a Moroko, inda Gabon ta kasa samun nasara a dukkan wasanni uku na rukuni da ta buga.
Ya zura kwallaye tara tare da taimakawa a ci biyar a gasar Ligue 1 ta bana.
Ademola Lookam - Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan tsakiyar na Najeriya wanda ya koma taka leda a Atletico Madrid na Sifaniya daga Atlanta, yana cikin jerin zaratan ƴan wasan Afrika da ba za su halarci gasar kofin duniya ba.
Lookman ya kasa taimaka wa ƙasarsa ne bayan kasa samun gurbi.
Sai dai, tun komawarsa Atletico, ya ci gaba da haska wa inda ya zura kwallaye bakwai da kuma bayar da taimakawa a ci huɗu.
Kuma yanzu haka ƙungiyarsa ta kai wasan daf da karshe na Champios League, inda aka tashi canjaras a wasan zagaye na farko da suka fafata da Arsenal ranar Laraba.
Sauran ƴan wasa
- Ola Aina - Najeriya.
- Carlos Baleba - Kamaru.
- Vincent Aboubakar - Kamaru.
- Yves Bissouma - Mali.
- Patson Daka Zambiya.
- Bertrand Traoré - Burkina Faso.
- Mbwana Samatta - Tanzaniya.








