Matar da ta yi wa ‘yan Taliban wa'azi riƙe da bindigogi kan amfanin ilimi

Asalin hoton, Adela
"Ban ji tsoro ba ko kadan, saboda na san abin da na yi a kan hanya yake,'' in ji matashiyar 'yar Afghanistan mai shekara 18 da babu alamar tsoro ko kadan tattare da ita.
Tana cike da burin ganin ta yi karatun jami'a, sai dai kash matakin gwamnatin Taliban ya sanya ta cikin matsananciyar damuwa saboda sun haramta wa mata zuwa jami'a.
Takaici da bakin cikin ganin mafarkinta na neman bin iska, da tasgaro da yi wa makomarta kafar ungulu, (mun sauya sunanta saboda dalilai na tsaro) ta dauki matakin yin zanga-zanga ita kadai a gaban jami'ar Kabul ta hanyar amfani da kalma daya daga Alkurani, wani lamari da ba safai ake gani ba.
Ranar 25 ga watan Disamba, Adela ta tsaya gaban babbar kofar shiga jami'ar dauke da allon da aka rubuta kalma daya ta harshen larabci- Iqra, ko kuma ''Karanta''. Musulmai sun yi imanin ita ce kalmar farko da Allah SWA ya fara saukar wa Annabi Muhammad SAW.
"Allah ya ba mu damar neman ilimi. Ya kamata mu ji tsoron Allah, ba 'yan Taliban da ke son kwace mana 'yancinmu ba,'' a hirarta da BBC.
Zanga-zanga mutum ɗaya

Asalin hoton, Adela
"Na san suna yi wa masu zanga-zanga ba dadi. Suna lakada musu duka, su shure su da ƙafa, suna amfani da makamai, suna amfani da feshin ruwa, sukan azabtar da su da wutar lantarki.
Amma duk da haka na tsaya a gabansu,'' in ji Adela lokacin hira da sashen BBC Afghanistan.
"Da farko ba su dauki abin nawa da muhimmanci ba. Amma daga baya wani dauke da bindiga ya ce na bar wurin."
A zahiri, Adela ta ki barin wurin, ta yi tsayuwar daka, amma a hankali kwalin da take dauke da shi da kalmar da ke jiki ta fara daukar hankalin mutanen da ke kusa da ita.
A daidai lokacin ta yi amfani da wannan dama, ta fara jan hankalin mutane ciki har da 'yan Taliban.
''Za ka iya karanta abin da aka rubuta?'' ta tambayi daya daga ciki. mma ya kasa cewa komai, don haka sai Adela ta ci gaba da magana; ''Yanzu ba za ka iya karanta kalmar Allah ba?''

Asalin hoton, Adela
"Ransa ya yi mugun ɓaci, daga nan ya fara yi min barazana." An ƙwace allon, an kuma tilasta mata barin wurin bayan mintuna 15 da fara boren nata.
A lokacin da take zanga-zangar, yayarta na zaune cikin wata taksi tana daukar hotuna da bidiyon abin da ƙanwarta ke yi.
"Direban taksi din ya fara jin tsoron 'yan Taliban. Yana ta rokon yayar ta daina daukar hotuna da bidiyon. Saboda a tsorace yake matuka, ya kuma ce ta fice masa daga mota."
Karuwar matsawa mata da yi musu iyaka
Janyewar dakarun kasashen waje da Amurka ke jagoranta, ba zato ba tsammani daga Afghanistan, ya bai wa Taliban damar karbe mulki da kasar a watan Agusta 2021."

Asalin hoton, AFP
Da farko sun haramta wa 'yan mata komawa makarantar Sakandire bayan kammala dogon hutu.
A watan Satumba, sun hana dalibai mata daukar wasu daga cikin darussa, sun kuma fada musu za su iya zabar jami'ar da ke kusa da gundumominsu.
Ranar 20 ga watan Disamba, suka haramta wa mata zuwa jami'a, lamarin da ya tunzura duniya da janyo alla-wadai, bayan kwanaki kadan suka kara daukar matakin hana mata zuwa wuraren aiki da kuma aiki da kungiyoyin agaji.
Mata musamman daliban jami'a sun yi ta zanga-zanga kan lamarin musamman wadanda ke da burin zurfafa ilimi.
Wasu daga ciki suna amfani da kalmomin ''mata, rayuwa, 'yanci.'' kamar yadda aka riƙa amfani da su a lokacin zanga-zangar baya-bayan nan a Iran.
Jami'ai a jami'ar Kabul, da hudu daga cikin tsangayoyin mata ne ke jagoranta, sun shaida wa BBC cewa an hana Farfesoshi mata shiga harabar jami'ar.
Kira ga mata

Asalin hoton, Getty Images
"Lokacin da na yi zanga-zangar, wani matashi ya so daukar hoto da bidiyo da ni domin ya karfafa min gwiwa. Amma 'yan Taliban suka lakada masa duka,'' in ji Adela.
Wani farfesa ya yaga takardun shaidar difiloma da ya yi, an kuma yada kai tsaye a talbijin domin nuna adawarsa, kuma wani makusancinsa ya shaida wa BBC cewa malaman jami'a sama da 50 ne suka ajiye aiki a wani bangare na nuna adawa da matakan.
Wani malami da ya ajiye aikin koyarwar, ya shaida wa BBC cewa ya janye matakin nasa, bayan mambobin Taliban sun lakada masa dan karen duka.
Amma Adela ta amince, lamari ne mai matukar wuya mazan Afghanistan su shiga wannan gwagwarmayar.
"Mazan Afghanistan tsiraru ne suka tsaya mana. A Iran maza sun fito domin gwagwarmaya a kan hakkin 'yar uwarsu, da ƙwatar wa mata hakki da 'yancinsu. Idan muka haɗa kai, muka yi tsayin daka domin kwato hakki da 'yancinmu na samun nagartaccen ilimi, to 100 cikin 100 nasarar tamu ce baki daya."
Ba gudu ba ja da baya

Asalin hoton, Getty Images
Sai dai shugabannin Taliban ko a jikinsu.Jaridar The Guardian ta Burtaniya ta ambato ministan Ilimi Nida Muhammad Nadim na cewa babu mai sauya matakin, ba gudu, ba ja da baya, ''ko da za su yi mana luguden makaman roka ne.''
Ita ma Adela ba ta karaya ba
"Idan ba zan iya tashi sama ba, ai zan iya fyalla gudu. Idan ba zan iya gudu ba, babu abin da zai hana ni tafiya cikin tsanaki.
Idan ba zan iya duka ba, tabbas zan ja ciki. Abu guda daya na sani, ba zan taba karaya ba, ba zan daina gwagwarmaya ba, sai inda karfi na ya kare.''
Kawayenta sun ba ta karin gwiwa, inda suke cewa - "ke gwarzuwa ce, kin amince matan Afghanistan za su iya komai a rayuwa, za kuma su iya kwatarwa kansu 'yanci, da samun ingantacciyar rayuwa.
"Ba ma fatan koma wa rayuwar kuncin da mukai a baya, shekara 20 da ta wuce. Mun fi lokacin baya ƙwarin gwiwa, mu ba ragwaye ba ne, muna da ilimi kuma mun san 'yancinmu.''











