Argentina ta ci gaba da zama ta ɗaya a jadawalin FIFA

Argentina

Asalin hoton, Getty Images

Zakarun ƙwallon ƙafa na duniya, Argentina, sun kare matsayinsu na ɗaya a jerin ƙasashen da suka fi ƙarfi a fagen ƙwallon ƙafa a duniya.

Cikin jerin ƙasashen da hukumar FIFA ta fitar ranar Alhamis, ya nuna cewa ƙasashe biyar na farko matsayinsu bai sauya ba.

Argentina, wadda ta tsige Brazil daga matsayi na farko a jaddawalin a watan Afrilu, ta ci gaba da zama a kan gaba bayan ta doke Ecuador da Bolivia a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya na 2026.

Faransa ta biyu, wadda ta sha kashi a hannun Jamus a wasan sada zumunci a makon da ya gabata, ta rike matsayinta na biyu inda Brazil ke bin ta a baya, Ingila ce ta huɗu sai Belgium a matsayi na biyar.

Portugal ce ta daya tilo a cikin kasashe 10 na farko da suka haura zuwa matsayi na takwas, yayin da Italiya ta sauko zuwa matsayi na tara bayan ta tashi 1-1 da North Macedonia a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai na 2024.

A kasashen Afrika kuwa Morocco ce kan gaba inda ta ke matsayi na 13 a duniya, sai Senegal ke biye da ita a matsayin ta biyu a Afrika amma ta 20 a duniya, Tunisia kuwa na matsayi uku a Afirka kuma ta 29 a duniya.

Najeriya da Kamaru ba su sauya matsayi ba inda suke na shida da na bakwai a Afrika kuma matsayi na 40 da 41 a duniya.