Abu goma da ya kamata mai azumi ya lazimta
Yayin da Musulmi suka fara azumin watan Ramadana, malamai sun lissafa waɗansu halayya guda 10 da ya kamata masu azumin su runguma a tsawon kwanaki 29 ko 30 na watan da ma bayan nan.
Sheikh Nuru Khalid, malamin addinin Musulunci a Abuja, wanda ya lissafa abubuwan goma, ya ce watan Ramadana makaranta ce da ake so daraussan da aka samu su ci gaba da kasancewa da mai azumi.








