Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ra'ayi Riga: Kan ɓullar ƙungiyar Lakurawa a arewacin Najeriya 15/11/24
Ra'ayi Riga: Kan ɓullar ƙungiyar Lakurawa a arewacin Najeriya 15/11/24
A 'yan makonnin baya-bayan nan ne aka samu ɓullar wata ƙungiyar 'yanbindiga da ake kira Lakurawa a yankin arewa maso yammacin Najeriya.
Ya zuwa yanzu sun kashe mutane da dama a jihar Sokoto makwabciyarta jihar Kebbi.
Sai dai Hukumomi sun ce mayaƙan sun zo a daidai lokacin da dakarun ƙasar ke cikin shirin kawar da duk wata barazana daga 'yanbindiga.
Su wane ne Lakurawa? Daga ina suke? Ta ya za a daƙile su?
Waɗannan na daga cikin batutuwan da shirin na wannan makon ya tattauna.