An dakatar da Pogba na tsawon shekara huɗu

Asalin hoton, Getty Images
An dakatar da ɗan wasan Juventus Paul Pogba daga buga ƙwallon ƙafa na tsawon shekara huɗu bisa samunsa da laifin amfani da sinadarai masu ƙara kuzari.
An dakatar da tsohon ɗan wasan na Manchester United na wucin-gadi a watan Satumba bayan wani gwajinn da aka yi ya gano sinadarin testosterone mai yawa a jikinsa.
An gwada Pogba ne bayan wasan farko na Juventus a gasar Serie A a ranar 20 ga watan Agusta.
An shaida wa BBC cewa Pogba zai daukaka ƙara kan hukuncin da hukumar hani da amfani da kwayoyi masu kara kuzari ta Italiya (Nado) ta yanke.
Hukuncin na nufin Pogba ba zai iya taka leda ba har sai shekarar 2027, lokacin da zai cika shekaru 33, bayan an tabbatar da cewa hukuncin zai fara aiki ne daga ranar da aka yi masa gwajin farko.







