Yadda sabuwar fasahar 'magana da mamaci' ke aiki

James Vlahos

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, James Vlahos ya fara tunanin irin wannan hanya ce bisa rajinsa na ci gaba da rayuwa da mahaifinsa wanda likitoci suka ce ya kusa mutuwa
    • Marubuci, By Egon Cossou
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Business reporter

A shekarar 2016 ne James Vlahos ya samu wani mummunan labari - cewar an gano mahaifinsa na fama da cutar sankara, wadda ta riga ta yi muni.

James, wanda ke zaune a garin Oakland, a jihar California na ƙasar Amurka ya ce: "Ina matuƙar son mahaifina, ga shi zan rasa shi."

Ya sha alwashin amfani da sauran lokacin da ya rage wa mahaifin nasa na rayuwa yadda ya kamata.

"Na zauna tare da shi inda ya ba ni tarihin rayuwarsa, na kwashe sa'o'i ina naɗar tarihinsa da yake ba ni da kansa."

Lamarin ya zo daidai lokacin da James ke ƙoƙarin shiga harkar ci gaban zamani ta Ƙirƙirarriyar basira, daga nan ne ya fara aikinsa.

"Sai na yi tunanin me zai hana na yi wani abu da wannan lokaci da na samu?" in ji shi.

"Domin na samu abun da zan riƙa tunawa da shi da kuma jin tamkar yana tare da ni."

Mahaifin James ya rasu a shekarar 2017, dab da lokacin da James ɗin ya samar da manhajar ƙirƙirarriyar basira wadda ke amsa tambayoyi kan rayuwar mahaifin nasa cikin muryarsa.

James Vlahos with his dad John

Asalin hoton, James Vlahos

Bayanan hoto, James Vlahos da mahaifinsa John
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masana kimiyya sun daɗe suna hasashen yadda za a iya ci gaba da amfani da wasu abubuwa na mutanen da suka mutu, to a yanzu ci gaban harkar fasasha ya sa mafarkin nasu ya zama gaskiya.

A 2019, James ya mayar da abin da ya ƙirƙira zuwa wata manhaja wadda ya raɗa wa suna 'HereafterAI', wato ƙirƙirarriyar basirar bayan mutuwa, wadda ke bai wa duk mai buƙata damar naɗa tare da amfani da muryar ƴan'uwansu ko bayan sun mutu.

Ya ce duk da cewa manhajar ba za ta cire masa damuwar rashin mahaifinsa ba amma ta samar masa abun da ba zai iya samu ba in da bai yi hakan ba.

Yayin da manhajar 'HereafterAI' ke bai wa masu amfani da ita damar sanya hoton ƴan'uwansu da suke so su fito a kan waya ko kwamfuta a lokacin da suke amfani da manhajar, wani kamfanin ƙirƙirarriyar basirar ya ƙara inganta lamarin.

Wani kamfanin sadarwar zamani da ƙirƙirarriyar basira a Koriya ta Kudu mai suna DeepBrain AI, yana samar da kwafin mutum (Avatar) bayan ɗaukar murya da bidiyon mutum na sa'o'i ta yadda zai ɗauki yanayin motsin fuskar mutum da sauaka da tashin muryarsu.

"Mukan samar da tamka ta surar mutum da kimanin kashi 96.%," in ji Michael Jung, shugaban sashen kuɗi na kamfanin DeepBrians AI.

Ya ƙara da cewa "ta yadda iyalan mamaci ba za su ji wani iri ba idan suna tattaunawa da hoton nasa, duk kuwa da cewa ba na gaske ba ne."

Kamfanin na da yaƙinin cewa wannan ci gaba ta fasaha za ta zamo wani ɓangare na abin da ya shafi mace-mace - inda za mu iya shiryawa kafin lokacin mutuwa, ta yadda za mu bar wani abu da za a ci gaba da "tunawa da mu har abada."

Tsarin yana da tsada, kuma ba kowa ne ke iya ƙirƙirar kwafen ɗan'uwan nasa ba, kamfanin ne ke yi.

Dangi kan biya kamfanin kuɗin da suka kai dalar Amurka 50,000 domin su aikin naɗar bidiyon ƴan'uwan nasu da kuma yin kwafen.

Duk da tsadar abin, wasu masu zuba jari na da yaƙinin cewa mutane za su karɓi tsarin, har ma kamfanin na DeepBrain ya tara kuɗi dalar Amurka miliyan 44 a gidauniyar da ya kafa.

Sai dai wata ƙwararriya kan halayyar ɗan'adam Laverne Antrobus ta ce ya kamata a yi taka-tsantsan wajen amfani da irin wannan fasaha a lokacin da mutane ke cikin jimami.

"Rashin wani namu abu ne da ke girgiza mutum, kada ya zama sai ka ni kamar ka kusa komawa daidai amma wani abu ya sake mayar da kai.

"Tunanin cewa za ka samu damar jin muryar wani naka da ya rasu ko kuma ka ji su suna magana lamari ne da zai iya sanya mutum cikin ruɗani."

Antrobus ta ƙara da cewa kada mutane su gaggauta rungumar wannan fasaha ta yin magana da kwafen ƴan'uwansu da suka mutu. "Dole ne ka zama mai ƙarfin rai kafin ka gwada yin haka. A bi abubuwa a hankali."

Deepbrain AI

Asalin hoton, Deepbrain AI

Bayanan hoto, Wata mata na taɓa hoto mai magana na wani tsoho da kamfanin DeepBrain AI ya haɗa

Kowane mutum na da yadda yake ji idan ya faɗa cikin damuwa, amma duk da haka akwai wasu abubuwan da kan faru da kowanne mutum idan yana cikin damuwa.

Bankuna da kamfanonin da shafukan sada zumunta na buƙatar mutane su cika wasu takardu domin rufe asusu ko shafukan sada zumunta na ƴan'uwa da suka mutu.

Vicky Wilson and her late grandmother

Asalin hoton, Settld

Bayanan hoto, Vicky Wilson da kakarta wadda ta mutu

Kamfanonin fasaha masu yin abubuwan da suka shafi jimamin mamata waɗanda ake kira "death tech" yanzu an ƙiyasta cewa suna da jarin da ya kai fam biliyan 100 a faɗin duniya, in ji shafin TechRound.

Shugaban shafin ya ce annobar korona ta taimaka wajen bunƙasar ɓangaren na fasahar zamani ta jimamin mamata.

Sai dai Ms Antrobus ta ja hankali kan cewa babu wani abu da zai samar wa mai jimamin mamaci sauƙi fiye da ɗan'adam.