Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hikayata 2024: Labarin Yi Wa Kai
Labarin Yi Wa Kai wanda Maryam Abdu'aziz da ke gida mai lamba 1498 Ɗandago, Titin Yar Maishinkafi, ƙaramar hukumar Gwale da ke birnin Kano ta rubuta wanda kuma ma'aikaciyar BBC Hausa Badriyya Ƙalarawi ta karanta.
YI WA KAI dai labari ne da ya ginu akan wata matar aure da ta yi saki na dafe da gwaggwaɓar damarta wadda wasu matan ke neman ta ido makance, bisa ruɗun zuciyarta da ya kasance ta gwamutsa ƙazamin tunaninta da na ƙawarta da ta riƙa tamkar zobe.
Al'amarin har ya kaita da yin saki reshe ta kama ganyen da ya wulwulota ya kwaɗa ƙeyarta da ƙasa.
Daga bisani ta fahimci lallai wasa ya ɓaci mai wasan tauri ya taka wuka, bisa lura da ta kai magaryar tukewar da babu damar waiwayawa baya balle ta gyara kuskurenta domin shi hannun agogo baya taɓa dawowa ya riga ya shuɗe, sai ga shi nadama tasa ta gane wannan ƙawarta ta ba kowa bace face lumbu-lumbu wutar ƙaiƙayi.