Ko Shirin samar da zaman lafiya na Trump zai zama barazana ga aikin MDD?

Shugaban Amurka, Donald Trump
    • Marubuci, Lyse Doucet
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Chief international correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 6

Shugaban Amurka, Donal Trump ya ce "Idan aka haɗa kai, ana iya kawo ƙarshen wahalhalun da aka ɗauki shekaru ana fama da su tare da dakatar da ƙiyayya da zubar da jini da suka daɗe suna faruwa, sannan a samar da zaman lafiya mai ɗorewa ga yankin da ma duniya baki ɗaya.

Trump ya faɗi hakan ne a taron tattalin arziƙi na duniya da aka yi a Davos, Switzerlanda lokacin da yake ƙaddamar da shirin samar da zaman lafiya ta duniya wadda ya ce zai taimaka wajen warware rikice-rikicen duniya.

Saboda yawan yaƙe-yaƙe da matsaloli da duniya ke fuskanta, mutane da dama suna fatan wannan kalaman na Trump ya zama gaskiya.

Sai dai kuma, masu sa ido kan harkokin duniya da jami'an gwamnati a ƙasashe daban-daban ba su yarda da hakan ba gaba ɗaya. Suna ganin wannan mataki wani yunƙuri ne na Trump na rusa tsohon tsarin hulɗar ƙasashen duniya da aka kafa bayan Yaƙin Duniya na Biyu, ya maye gurbinsa da sababbin tsare-tsare da shi kansa zai fi rinjaye da iko a cikinsu.

Firaministan Poland, Donald Tusk, ya nuna shakku da taka-tsantsan, inda ya ce ƙasarsa ba za ta bari a yaudare ta ko a yi amfani da ita ba.

...

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An samar da wannan shiri na samar da zaman lafiya ta duniya ne tun a bara, a ƙoƙarin da Amurka ta jagoranta na kawo ƙarshen yaƙin Gaza, kuma Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da shi.

Sai dai babban mai goyon bayan Trump a Turai, Firaministan Hungary Viktor Orban, ya yabawa shirin.

Orban ya bayyana cikakken goyon bayansa inda ya ce: "Idan Trump ne, to zaman lafiya ne."

Amma kuma wannan shirin na Trump ya haifar da tambayoyi kamar haka, mene ne ainihin aikin wannan Hukumar Zaman Lafiya wadda Trump ɗin da kansa zai jagoranta? Me za ta yi dabam da sauran ƙungiyoyin duniya da ke kula da zaman lafiya ke yi?

Ƙarfin shugaban shirin

Wannan shiri na samar da zaman lafiyata duniya ya samo asali ne tun a bara, a ƙoƙarin da Amurka ta jagoranta na kawo ƙarshen yaƙin Gaza, kuma Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da shi.

Amma yanzu an faɗaɗa shi zuwa babban shiri na duniya.

Bisa bayanan da suka fito daga kundin shirin samar da zaman lafiya, Trump zai zama shugaban shirin na dindindin, ko da ya bar mulkin Amurka.

Trump zai samu cikakken iko, ciki har da zaɓen ƙasashen da za su shiga ko a'a da kuma naɗa wanda zai gaje shi a duk lokacin da ya ga dama.

Duk ƙasar da ke son zama mamba na dindindin na shirin, dole ta biya dala biliyan 1.

Wannan ya zo ne a cikin wani lokaci mai cike da manyan abubuwa da suka faru kamar kama shugaban Venezuela da Amurka ta yi, barazanar Trump na kai hari Iran, da kuma buƙatar Amurka ta mallakar Greenland lamarin da ya girgiza Turai da sauran duniya.

Shugaban Amurka, Donald Trump

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, "Da zarar an kammala kafa wannan shirin, za mu iya yin kusan duk abin da muka ga dama tare da Majalisar Ɗinkin Duniya." in ji Trump
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ƙasashe 19 ne suka halarci taron ƙaddamar da shirin a Davos, daga sassa daban-daban na duniya, ciki har da Argentina da Azerbaijan da tsoffin ƙasashen Tarayyar Soviet da kuma ƙasashen Gulf.

An ce wasu ƙasashe da dama sun riga sun amince za su shiga shirin.

Trump ya nuna farin ciki, yana cewa yana son dukkan shugabanni da jami'an da suka shiga shirin.

Sai dai ƙasashe da dama sun nuna shakku.

Birtaniya ta ce akwai batutuwa da dama a ƙasa kuma sun nuna damuwa kan yadda Rasha ƙarƙshin shugaba Putin za ta kasance cikin wannan shiri na zaman lafiya.

Trump ya ce Rasha na cikin shirin, amma Moscow ta ce har yanzu suna tuntubar abokan hulɗarta.

Sweden ta ce ba za ta shiga shirin ba yayin da Norway ta ce har yanzu akwai tambayoyi da ke buƙatar ƙarin tattaunawa da Amurka.

Wasu ƙasashen Musulmi, ciki har da ƙasashen Larabawa da Turkiyya da Indonesia, sun ce sun shiga ne don neman adalci da zaman lafiya mai ɗorewa a Gaza da sake gina yankin.

Sai dai bayanan da suka fito daga shirin, ba a ambaci Gaza ba kwata-kwata.

Zauren MDD

Asalin hoton, Reuters

Wasu masu sukar wannan shiri, ciki har da ƙasashen da ba su son shiga, na ganin cewa wannan aikin nuna girman kai ne na Shugaba Trump, wanda ke da burin samun babbar lambar yabon zaman lafiya ta Nobel wadda Barack Obama ya samu a 2009.

Shugabannin duniya sun fahimci cewa idan suka ƙi amincewa su shiga wannan shirin, toh za su iya ɗanɗana kuɗarsu.

Trump ma ya yi barazana ga Faransa, inda ya ce zai lafta mata haraji mai tsanani kan barasa na ƙasar idan Shugaba Emmanuel Macron bai shiga ba shirin ba.

Slovenia ce kaɗai ta faɗi damuwarta kai tsaye, tana cewa wannan shirin na iya lalata tsarin hulɗar ƙasashen duniya da ake da shi.

Trump ya mayar da martani kan wanna damuwa, yana mai cewa da zarar an kammala kafa shirin, za su iya yin kusan duk abin da suka ga dama tare da Majalisar Ɗinkin Duniya.

A lokacin da gidan Talabija na Fox ta tambaye Trump ko wannan shirin na sa zai iya maye gurbin Majalisar Ɗinkin Duniya, sai ya ce "toh, killa zai iya" yana mai cewa MDD ba ta cika ƙarfinta ba wajen warware rikice-rikicen duniya.

Majalisar Ɗinkin Duniya mai mambobi 193 ta daɗe tana take takawa a matsayin babbar mai sasanta zaman lafiya a duniya. Tun lokacin da António Guterres ya zama Sakatare-Janar a 2016, ya yi alƙawarin ƙara ƙoƙarin diflomasiyya domin zaman lafiya, amma hakan bai yi tasiri sosai ba.

A tsawon shekaru goma da suka gabata, aikin MDD ya ci tura saboda rikicin ra'ayi a Kwamitin Tsaro da yawaitar ƙasashen da ke tayar da rikice-rikice, da kuma raguwa a tasirinta a idon manyan ƙasashe kamar Amurka.

Tsohon jami'in MDD, Martin Griffiths, ya ce ya dace a yaba wa Trump kan ƙoƙarinsa na kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe, amma ya jaddada cewa wannan sabon yunƙuri alama ce ta gazawar Kwamitin Tsaron MDD.

Sai dai ya yi gargaɗi cewa zaman lafiya na gaskiya na buƙatar haɗa kowa, ba ƙawayen Trump kaɗai ba.

Guterres ma ya nuna damuwa, yana cewa wasu na ƙoƙarin maye gurbin ikon doka da ikon ƙarfi.

Game da iƙirarin Trump na cewa ya kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe takwas, Guterres ya ce abin da aka samu dai tsagaita wuta ne kawai, kuma wasu daga cikin yarjejeniyoyin sun riga sun rushe, kamar a Rwanda da DR Congoda Cambodia da Thailand, da kuma rikicin Indiya da Pakistan, inda aka ƙi amincewa da rawar da Trump ya taka.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu

Wasu na ganin cewa shiga tsakani da Trump ya yi ya ne ya sa aka kawo ƙarshen yaƙin kwanaki 12 tsakanin Iran da Isra'ila.

Haka kuma, shiga tsakani kai tsaye da ya yi ne ya haifar da tsagaita wuta a Gaza a watan Oktoban da ya gabata, wanda ya rage wahalar Falasɗinawa tare da sassauta raɗaɗin iyalan fursunonin Isra'ila.

An ce Trump ya mai da hankali sosai kan rikicin ne bayan matsin lamba daga ƙawayensa na Larabawa da iyalan Isra'ilawa da ke cikin jimami, lamarin da ya sa ya matsa wa Firaministan Isra'ila Netanyahu da kuma Hamas sun cimma yarjejeniya.

Sai dai ƙalubalen farko na wannan sabuwar shirin samar da zaman Lafiya shi ne yadda za a ci gaba daga matakin farko na yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin Gaza gaba ɗaya.

Matsalar ita ce, hukumar ta haɗa Netanyahu, wanda ya ƙi yarda da amincewa da kafa ƙasar Falasɗinu, da kuma shugabannin Larabawa da ke cewa babu zaman lafiya mai ɗorewa sai an bai wa Falasɗinawa ikon cin gashin kansu kuma an kawo ƙarshen mamayar Isra'ila.

A gefe guda kuma, akwai rikicin Ukraine, inda Shugaba Zelensky ya ƙi zama a tebur ɗaya da Rasha da Belarus.

A ƙarƙashin wannan shiri, akwai wasu matakai uku, galibinsu kan Gaza, ciki har da Kwamitin Zartarwa da Kwamitin Kula da Gaza, waɗanda suka haɗa manyan jami'an Amurka da attajirai da tsoffin 'yan siyasa da tsoffin jami'an MDD da shugabannin tsaro na Larabawa da kuma ƙwararrun Falasɗinawa.

...

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Gaza

Ko da wasu masu sukar Trump suna da ra'ayi, an yaba masa cewa ya jawo hankali kan wani tsohon matsala wanda ya haɗa da bukatar sauya tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya musamman Kwamitin Tsaro wanda ba ya wakiltar manyan ƙasashe yadda ya kamata a kowace yanki.

Mark Malloch Brown, tsohon mataimakin sakataren MDD, ya ce wannan na iya dawo da wannan batu a saman manufar duniya.

Trump na ƙoƙarin jagorantar zaman lafiya ne a lokacin da ake shirin maye gurbin sakataren MDD, António Guterres, a ƙarshen wannan shekara. Duk da cewa ya taɓa cewa zai kawo ƙarshen yakin Ukraine a rana guda, ya fahimci cewa kawo zaman lafiya tsari ne mai wahala.