Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Wane irin motsa jiki ne ya dace da mai juna biyu?
Motsa jiki mara ƙarfi na da kyau ga mace mai juna biyu, musamman wajen yin goyon ciki da kuma wajen naƙuda, a cewar hukumar lafiya ta burtaniya.
Haka kuma yana taimaka mata wajen daidaita ƙibarta a lokacin goyon ciki.
Hukumar ta zayyana wasu nau'ukan motsa jikin da ta ce za su dace da mai juna biyu.
Wasu daga ciki sun haɗa da tattaki, yin tafiya abu ne mai kyau ga mai ciki, musamman ma wadda bata saba yin motsa jikin ba gabanin samun jikin.
Ninƙaya, lanƙwasa ko miƙe gaɓoɓi, motsa jiki don kwankwaso da mara na daga cikin ire-iren motsa jikin da hukumar ta ce suna da kyau ga masu ciki.
Sai dai hukumar ta ja hankali ga masu juna biyu kan wasu nau'ukan motsa jikin da ta ce basu da ce ba ga mai ciki.
Sun haɗa da wanda zata kwanta a rigingine, musamman idan cikinta ya haura makonni 14.
Ko duk wani motsa jiki da zai sa ta buge cikinta ko motsa jiki mai ƙarfi.
Dr. Saliha Muhammad, wata likitar mata kuma jami'a a ma'aikatar lafiya a jihar Kaduna da ke Najeriya, ta yi ƙarin bayani kan tasirin motsa jiki ga mai ciki.
Latsa makunnin da ke sama domin jin shirin lafiya zinariya kan wannan batu.