Yadda ake amfani da sauro wurin yaki da maleriya a Djibouti

Asalin hoton, Oxitec company
- Marubuci, Dorcas Wangira
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC kan lafiya
An saki dubun dubatar saurayen da aka sauya wa ƙwayoyin halitta a ƙasar Djibouti da zimmar daƙile yaɗuwar saurayen da ke yaɗa cutar maleriya.
Saurayen Anopheles maza ne da ba su cizo, waɗanda kamfanin Birtaniya Oxitec ya ƙirƙira kuma suna ɗauke da wata ƙwayar halitta ne da ke kashe matan cikinsu tun kafin su balaga.
Da ma dai sauraye mata ne kawai ke cizo kuma suke yaɗa maleriya da sauran cutuka.
Wannan ne karo na farko da aka saki saurayen a yankin Afirka ta Gabas kuma karo na biyu a faɗin nahiyar baki ɗaya.
An yi amfani da irin wannan fasahar cikin nasara a Brazil, da Cayman Islands, da Panama, da Indiya, a cewar hukumar kare yaɗuwar cutuka ta Amurka Centre for Disease Control and Prevention (CDC).
An saki irin wannan saurayen sama da biliyan ɗaya a faɗin yankin Ambouli da ke birnin Djibouti ranar Alhamis.
Aikin gwaji ne tsakanin Oxitec Ltd, da gwamnatin Djibuti, da kuma ƙungiyar Association Mutualis.
"Mun ƙirƙiri saurayen da ba su cizo, ba su yaɗa cuta. Idan muka saki waɗannan sauraye, za su yi mu'amala da matan," kamar yadda shugaban Oxitec ya faɗa wa BBC.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Saurayen da aka samar a ɗakunan gwaji na ɗauke da "ƙwayar halittar da ke hana" jariransu mata girma da zarar sun yi mu'amala tare.
Mazansu ne ke tsira amma daga kuma su mutu, a cewar masana kimiyyan da suka yi aikin.
Ba kamar sauraye maza na Anopheles colluzzi da aka saki a Burkina Faso a 2018, saurayen na yanzu masu suna stephensi za su iya saka ƙwai.
Tun shekara biyu da suka wuce aka fara gwajin sakin saurayen waɗanda aka fara ganowa a 2012.
A lokacin, ƙasar na ƙoƙarin kawo ƙarshen maleriya. Tun daga lokacin kuma zazzaɓin na maleriya ya dinga ƙaruwa sosai zuwa 73,000 a 2020.
Yanzu akwai irin waɗannan sauraye a ƙasashen Afirka shida - Habasha, Somaliya, Kenya, Sudan Najeriya, Ghana.
Nau'in sauro na stephensi da suka samo asali a nahiyar Asiya, na da wuyar sha'ani. Kazalika akan kira shi da sauron cikin birni da ya gagari magani. Yakan ciji mutum da rana da kuma dare.
Wani mai bai wa gwamnatin Djibuti shawara, Dr Abdoulilah Ahmed Abdi, ya faɗa wa jaridar Financial Times cewa burin gwamnatin shi ne "daƙile maleriya cikin gaggawa a ƙasar, wanda ya ƙaru cikin shekara 10 da suka wuce".
"Ba da daɗewa ba, maleriya ta yi ƙaranci a garuruwanmu," in ji shugaban Association Mutualis Dr Bouh Abdi Khaireh.
"Yanzu kuma muna ganin marasa lafiya kusan a kullum a faɗin Djibuti. Akwai buƙatar ɗaukar ƙarin matakai."

Asalin hoton, Oxitec company
An daɗe ana cecekuce kan halittun da ake sauya wa ƙwayoyin halitta a Afirka. Masu rajin kare muhalli sun yi ta gargaɗin abin da hakan zai iya haifar wa muhalli da kuma samar da abinci.
Amma Mista Frandsen na Oxitec ya ce wannan aikin ba shida wata matsala da muhalli ko lafiyar ɗan'adam da aka taɓa samu cikin shekara 10 - lokacin da kamfanin ya saki biliyoyin sauraye da aka sauya wa ƙwayar halitta.
"Wannan sabon salon zai iya jawo cecekuce amma kuma shi ne makomarmu," a cewar Dr Abdi.
Idan tsarin ya yi nasara, za a faɗaɗa girman gwajin, inda za a ci gaba da sakin ƙarin sauraye har zuwa cikin shekara ta gaba a ƙasar.
Maleriya cuta ce mai haɗari da ke kashe aƙalla mutum 600,000 duk shekara a faɗin duniya. Mutum ɗaya cikin 10 da cutar ke kashewa na Afirka, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya.











