Yadda jami'an tsaro suka shiga gidan shugaban ƙasar Koriya ta Kudu suka kamo shi

Asalin hoton, Reuters
Yoon Suk Yeol ya zamo shugaban ƙasa na farko mai ci da aka taɓa tsarewa a Koriya ta Kudu bayan da jami'ai masu bincike suka kawar da shinge da karya wayar da ta kange gidan domin su kamo shi.
Ana binciken Yoon mai shekaru 64 ne dai bisa tuhumar tayar da tarzoma a ƙasar bayan da ya gaza sauya dokokin ƙasar da na tsarin mulkin soja a watan Disambar 2024 wani abu da ya jefa ƙasar cikin ruɗani.
Da ma dai majalisar dokokin ƙasar ta riga ta tsige mr Yoon daga kuerar shugaban ƙasar to sai dai za a iya tunɓuke shi daga kan kujerar ne kawai idan kotun tsarin mulkin ƙasar ta amince da tsigewar.
To amma tsare mista Yoon ɗin na ranar Laraba ya kawo ƙarshen makonni biyu da aka kwashe ana zaman tankiya tsakanin masu binciken da masu tsaron lafiyar shugaban ƙasa.
Masu binciken dai daga sashen bincikenlaifukan rashawa da cin hanci sun gaza kama shugaban ƙasar a ranar 3 ga watan Janairu sakamakon kwashe awanni shida suna tataɓurza da dakarun shugaban ƙasar.
Da asubar ranar Laraba ne kuma tawagar masu binciken ta samu ɗauki ta hanyar ƙara yawansu inda suka kai mutum dubu ɗaya tare da ƴansanda suka yi dirar mikiya a gidan shugaban ƙasar da ke tsakiyar birnin Seol, inda suka yi amfani da tsanuka wajen hawa katangar gidan da wasu manyan motoci da suka yi musu shinge daga tarar da shugaban.
Kuma bayan kwashe awanni, sai hukumomi suka sanar da cewa an kama mista Yoon.
A wani bidiyo mai tsawon minti uku da aka wallafa, mista Yoon ya ce zai bayar da hadin kai dangane da binciken da ake yi masa duk da dai ya ce kama shi da binciken da ake yi masa ba halattattu ba ne.
Lauyoyin mista Yoon sun ce tsarewar ta saɓa dokokin ƙasar. To sai dai kotun ƙolin ƙasar ta ce tsarewar an yi ne bisa doka.
A yanzu haka dai ministan kuɗin ƙasar, Choi Sang-mok ne ke riƙon ƙwaryar jagorancin ƙasar sakamakon tsige mataimakin shugaban ƙasar na farko, Han Duck-soo da majalisar dokokin ƙasar - da ƴan hamayya suke da rinjaye, ta yi
Wace dama Yoon ke da ita?
Bisa tsarin sammaci, masu binciken ka iya riƙe mista Yoon har tsawon awanni 48, kuma daga nan ne suke buƙatar samun sabon sammaci na ci gaba da tsare shi domin ci gaba da bincike.
Idan aka samu wannan sammaci, to za su iya ci gaba da tsare shi har tsawon ƙarin kwana 20 kafin a gurfanar da shi a gaban kuliya.
Idan kuma ba a samu sabon sammacin ba to dole ne a sake shi bayan ƙarewar awanni 48 ɗin.
Magoya bayan mista Yoon dai na ci gaba da gudanar da zanga-zanga domin nuna ƙin amincewarsu da kamun nasa.
Sun yi dandazo a gaban gidansa tun kafin asubahin ranar Laraba, inda suka kasance daura da masu hamayya da shi.
Waiwaye
Ƙasar Koriya ta Kudu dai ta yi fama da matsalolin siyasa tun bayan da sanar da sauya dokar ƙasar da ta mulkin sojoji a ranar 3 ga watan Disamban 2024 wanda ya janyo ƴan majalsiar dokoki suka tsallaka katanga yayin shiga majalisa domin ƙin amincewa da dokar.
Shugaban ya ce yana kare ƙasar ne daga wasu mutane da ke kishiyantar ƙasar da ke goyon bayan Koriya ta Arewa, amma kuma ba jimawa sai ta bayyana cewa burinsa na siyasa ne ya haifar da hakan.
Shi dai Mista Yoon ya kasance shugaban ƙasan da ba shi da kataɓus tun bayan da ƴan hamayya suka lashe babban zaɓen ƙasar da aka yi a watan Afrilu da gagarumar nasara.











