Mutum 179 ne suka mutu a haɗarin jirgin sama a Koriya Ta Kudu

Asalin hoton, Reuters/Yonhap
Hukumomi a Koriya ta Kudu sun ce mutum 179 ne suka mutu a hatsarin jirgin saman da ya auku a filin jirgin saman Muan ranar Lahadi da safe.
Mutum biyu kawai aka samu cetowa daga hatsarin - waɗanda dukkansu ma'aikatan jirgin ne da aka zaƙulo daga cikin baraguzan jirgin.
Hakan na nufin duka fasinjojin jirgin 175 haɗe da ma'aikatansa hudu sun mutu a hatsarin.
Jirgin ya kauce daga titinsa yayin da yake sauka a filin jirgin sama a Koriya ta Kudu.
Jirgin ƙirar Boeing 7-3-7 ya sauka kenan, bayan dawowa gida daga Bangkok na kasar Thailand, dauke da fasinjoji 175 da ma'aikatansa shida.
Saukar ta sa ke da wuya ne ya kwace ya saki titinsa ya kutsa ta cikin wani gini, kana ya kama da wuta.
Shaidu sun ce sun ji karar fashewar wani abu mai karfi bayan faruwar lamarin.
Wasu ɓangarorin jirgin sun ƙone ƙurmus yayin da baƙin hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniyar inda lamarin ya faru.
Har yanzu ba a san musabbabin faɗuwar haɗarin ba, amma kafofin watsa labaran cikin gida na bayar da rahoton cewa mai yiwuwa tsuntsaye ne suka shige cikin injin jirgin suka haifar masa da matsala.
Shugaban ƙasar na riƙo ya aike da saƙon jaje ga 'yan ƙasar, tare da alƙawarta gudanar da bincike.
Hukumar sufurin ƙasar ta sanar da jigilar mutane a jiragen ƙasa kyauta zuwa wurin da lamarin ya faru.
Iyalai da 'yan'uwan waɗanda lamarin ya shafa sun yi cincirindo a wajen filin jirgin saman cike da faragabar rasa 'yan'wansu.
'Masu kula da filin jirgin sun buƙaci direban ya jinkirta sauka saboda tsuntsaye'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Jami'an hukumar sufurin Koriya ta Kudu sun bayar da bayanai kan abin da ya faru da jirgin yayin da ya doshi filin sauka.
Da farko jirgin ya yi yunƙurin sauka, amma sai masu kula da filin jirgin ta aike masa saƙon ya jinkirta sakamakon tsuntsaye da ke shawagi a titin da zai sauka.
Minti biyu bayan gargaɗin da aka aike wa jirgin, sai direban ya yi kiran gaggawa ga masu kula da filin, inda ya buƙaci sauka, amma ta ɗaya gefen.
Bayan samun damar ne kuma direban ya kuma sauke jirgin.
Bidiyon saukar jirgin ya nuna yadda ya sauka ba tare da tayoyi ko wani abu da ke taimaka wa saukar jirgi ba, lamarin da ya sa ya kauce wa hanyar har ya je ya bugi wani gini kafin ya kama da wuta.
Ma'aikatar sufurin ƙasar ta ce direban jirgin ya jima yana tuƙin jirgin sama tun 2019, yayin da ya shafe fiye da sa'o'i 9,800 yan tuƙa jirgin sama.
Tuni dai kamfanin da ya mallaki jirgin saman ya aike da saƙon neman afuwa da iyalan mutanen da lamarin ya rutsa da su.
Wannan haɗarin jirgin sama na faruwa ne kwanaki kadan bayan wani makamancinsa da ya faru da wani jirgin saman Azerbaijan, da ya janyo mutuwar mutane 38, da jikkatar wasu da dama.












