Messi ba zai buga wa Argentina gasar Olympics ba

Lionel Messi

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Messi ya ce shekarunsa sun wuce lokacin da zai buga kowace gasa

Tauraron ɗan wasan Argentina Lionel Messi ya ce ba zai shiga cikin tawagar ƙasarsa ta 'yan ƙasa da shekara 23 ba yayin gasar wasanni ta Olympics.

A madadin haka, Messi mai shekara 37 zai mayar da hankali kan buga gasar Copa America da za a fara a watan nan.

"Na faɗa wa kociya Mascherano kuma gaskiya mun fahimci matsalar," kamar yadda Messi ya faɗa wa kafar yaɗa labarai ta ESPN.

"Da wuya [mutum ya dinga tunanin Olympics yanzu] saboda Copa America ne a gabanmu. Zai zama wata biyu ko uku zan yi ba tare da ƙungiyar [Inter Miami] ba kenan, kuma yanzu shekaruna sun wuce a ce na shiga komai da komai.

"Ya kamata na duba da kyau, abin zai yi yawa idan na buga gasa biyu a jere. Na yi sa'a sosai da na buga Olympics kuma na lashe gasar tare da Mascherano."

Argentina da Messi za su fara kare kofin Copa America da suka ɗauka a gasar da ta gabata kuma za su fara wasa da Canada a ranar 20 ga watan Yuni. Za a buga wasan ƙarshe na gasar ranar 14 ga watan Yuli, kwana 10 kacal kafin fara Olympics ɗin a birnin Paris na Faransa.

Tun bayan da matasan na Argentina suka yi nasarar samun gurbi a Olympics aka fara yaɗa labarai cewa Messi zai shiga cikinsu a matsayin ɗaya daga cikin 'yan wasa uku masu shekaru da yawa kamar yadda doka ta bai wa kowace tawaga dama.

Mascherano ya ce ƙofar Messi a buɗe take ta shiga tawagar, kodayake dai ya amince da abubuwan da ke gaban ɗan wasan mai kambin gwarzon ɗan ƙwallon duniya bakwai.