Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gane Mani Hanya kan kula da sha’anin alamjirai da tsangaya a Najeriya,
Kwararar almajirai zuwa birane wani batu ne da yanzu haka ke ci wa gwamnatin Najeriya tuwo a kwarya musamman a daidai lokacin da kididdiga daga hukumomi da kungiyoyi daga gida da waje ke fallasa Najeriya dangane da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
Wasu alkaluma da Hukumar Raya Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta fitar a baya-bayan nan sun nuna Najeriya na da yara fiye da miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta duk da cewa hukumar ilimin firamare ta Najeriyar ta ce alkaluman miliyan 10 ne da doriya.
Shugaban hukumar da ke kula da sha’anin alamjirai da tsangaya ta Najeriya, Hon Sha’aban Sharada ya ce sun dukufa wajen ganin sun rage yawan alkaluman kamar yadda ya shaida wa abokin aikina, Haruna Ibrahim Kakangi.