Ramos zai iya komawa La Liga, Bournemouth na neman £100m kan Scott

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon gwarzon ɗan wasan Spain da Real Madrid, Sergio Ramos, mai shekara 40, na iya komawa ƙungiyar Getafe ta Madrid a wani mataki da ba a yi tsammani ba, kasancewar yanzu ɗan wasan baya ba shi da kwangila da wata ƙungiya. (Sport)
Bournemouth na iya neman fiye da fam miliyan 100 kan ɗan wasan tsakiya ɗan ƙasar Ingila, Alex Scott, mai shekara 23, wanda Chelsea da Liverpool ke nuna sha'awar ɗaukar sa. (Football Insider)
Ɗan kasar Jamus Florian Wirtz, mai shekara 23, ba shi da niyyar barin Liverpool, duk da cewa akwai rahotannin da ke nuna sha'awar Chelsea — ƙungiyar da tsohon kocinsa a Bayer Leverkusen, Xabi Alonso, ke jagoranta. (CaughtOffside)
Tottenham na ci gaba da sa ido kan ɗan wasan gaba ɗan ƙasar Jamus da ke buga wa Eintracht Frankfurt wasa, Younes Ebnoutalib, mai shekara 23. (TeamTalk)
Newcastle United na bibiyar ɗan wasan tsakiya na Valencia mai shekara 19, David Otorbi. (Marca)
Tottenham na sha'awar ɗaukar ɗan wasan tsakiya ɗan ƙasar Japan, Yuito Suzuki, mai shekara 24, daga Freiburg, yayin da Roberto de Zerbi ke ƙoƙarin ƙarfafa tawagarsa. (Fussball News)
Barcelona na sa ido kan ɗan wasan baya na Benfica, Daniel Banjaqui, mai shekara 18, amma za su iya fuskantar hamayya daga ƙungiyoyin Premier League, wato Newcastle da Manchester United.(Ekrem Konur)
Barcelona na fuskantar gasa daga Real Madrid wajen neman ɗan wasan baya na Stuttgart, Finn Jeltsch, mai shekara 20, yayin da Liverpool ma ke nuna sha'awa kan matashin ɗan wasan na Jamus. (Sport)
Arsenal da Tottenham na sa ido kan matashin ɗan wasan Barcelona, Xavi Espart, mai shekara 19, amma farashin da aka sanya kan ɗan wasan na Spain zai iya zama cikas a gare su. (CaughtOffside)


























