Jami'an gwamnatin Boris Johnson fiye da 42 sun yi murabus

Boris Johnson

Asalin hoton, PA

Ministocin gwamnati a Birtaniya sun shafe daren Laraba suna ganawa da Firaminista Boris Johnson a fadarsa, gida mai lamba 10 Titin Downing - domin su lallaba shi ya sauka daga mukaminsa.

Hakan na zuwa ne a yayin da sauran goyon bayan da yake da shi a jam'iyyar Conservative mai mulkin kasar ke raguwa.

BBC ta gano cewa daya daga cikin makusantansa - Sakatariyar harkokin cikin gida Priti Patel - na cikin wadanda ke lallaba shi ya yi murabus.

Ɓatawa da wasu na hannun bayansa

Mista Johnson dai ya kori Michael Gove, daya daga cikin manyan ministocinsa, wanda a baya ke kare gwamnatinsa amma a yanzu ya juya masa baya.

Sam Freedman, wani tsohon mai bai wa Mista Gove shawara yayin da yake karamin minista na ilimi ya bayyana mamakinsa ga yadda Mista Johnson ke mayar da martani.

Bayan da mutum 42 suka ajiye mukami, korar wani mutumin na daban ya yi kama da rashin dabara.

Sai dai abin mamakin shi ne ya kori Gove ne - mutumin da suka shaƙu kuma suka daɗe tare, kuma wannan alama ce ta yadda ikon Mista Boris ke ƙara rugujewa ta kowane ɓangare.

Duk da ajiye mukamai da jami'an wannan gwmanatin ta Birtaniya suka yi, ciki har da ajiye mukamin da manyan ministoci biyu suka yi, Mista Johnson ya kafe cewa ba zai miƙa wuya ba.

Sakataren kiwon lafiya Sajid Javid da sakataren baitulmali Rishi Sunak ne suka kunna wutar wannan rikicin na siyasa bayan da suka ce sun gane firaministan ba zai iya sauke nauyin da al'ummar Birtaniya suka dora masa ba.