Ku San Malamanku tare da Sheikh Ibrahim Maqari (Maimaici)

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Ku San Malamanku tare da Sheikh Ibrahim Maqari (Maimaici)

Fitacce malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya Sheik Ibrahim Ahmad Maqri ya ce babban abin da ya sanya a gaba shi ne samar da makarantu ko zawiyyoyi ko masallatai wadanda za su dace da tsari na wannan karni.

Malamin, wanda ɗaya ne daga cikin limaman babban masallacin Juma'a na Abuja, ya faɗi hakan ne a hirar da ya yi da BBC Hausa a shirinmu na musamman mai taken ''Ku San Malamanku''.

"Babu abin da na sanya a gaba illa kokarin yadda za mu samar da tsari na institution na addini. Idan an ce institution, ana nufin makarantu, ana nufin zawiyyoyi, ana nufin masallatai wadanda za su zama mu'assasat wadanda suka dace da zamanin da muke ciki, karni na ashirin da daya da kalubalen da ke cikin karni na ashirin da dayan, kuma su rika ba da gudunmawarsu a wannan tsari," in ji shi.

Ya kara da cewa muhimmin abu shi ne kada tsarin addini ya dogara da mutum daya.

A lokacin da aka yi wannan tattaunawa cikin shekarar 2021, malamin ya ce ko da yake bai taba tsayawa ya kirga adadin littafan da yake rubutawa ba amma "za a iya cewa za su kai arba'in."

Wane ne Sheikh Ibrahim Maqry?

An haifi Sheikh Ibrahim Ahmad Maqary a garin Zaria cikin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya a shekarar 1976.

Sheikh ya bayyana cewa ya fara karatunsana firamare a garin Katsina bayan da aiki ya mayar da mahaifinsa can.

''Kakana wanda ya haifi mahaifina shi ya zo kasar Zaria daga garin Borno da niyyar neman ilmi, kuma bayan ya samu abin da yake so ya bukaci ya koma inda ya fito don ya cigaba da ilmantar da al'umma,'' in ji Sheik Maqary.

Ya kuma ce "amma sai sarkin Zazzau na wancan lokacin ya ce ai shi malamai ba sa zuwa garinsa su bar garin, don haka sai ya ba shi gida ya ci gaba da zama yana ilimantarwa."

Malamin ya ce ya yi karatu gwargwado a gidan shahararren malami a garin Katsina Sheikh Abba Abu.

Ya kuma ce malaman da ya zauna da su don daukar karatu a garin Zaria suna da yawa, cikin su akwai malam Tanimu Kusfa, shahararren malamin fiqihu da sauran fannonin ilimi.

Sannan akwai babban malami a Zaria, Malam Bala Kusfa a wannan lokacin "kanin mahaifina yana daga cikin almajiransa, don haka yana daukarsa yana kai shi zaurensa don sauraron karatun."

Kafin tafiyarsa kasar Masar ƙaro ilimi, Sheikh Maqary ya hadu da daya daga cikin malaman da suka fi yin tasiri a rayuwarsa, Sheikh Muhammadu Amin Abdullahi mutumin Okene.

Malamin ya ce a kasar Masar babban guzirin da zai iya cewa ya samu shi ne haduwarsa da babban malaminsa, abin alfaharinsa a dukkan fannonin karatu da rayuwarsa Sheikh Ibrahim Saleh al-Hussaini.

Ya je kasar Masar karatu a daidai lokacin da ya bude makaranta.

Yawanci malamansa ba 'yan Najeriya ba ne, sun zo daga kasashen Mauritania da Morocco, don haka ya yi amfani da wannan damar wajen daukar wasu fannoni daga cikin ilimi daga hannun malaman.

Haddar Al-Ƙur'ani mai girma

Malamin ya ce yana da kimanin shekara 13 zuwa 14 ya yi haddar AlKur'ani a makarantar gidan Sheik Yahuza da ke birnin Zazzau.

A wannan lokacin ne ya samu babban sauyi a rayuwarsa, bayan da mahaifinsa ya cire shi daga tsarin karatun boko bayan ya kammala makarantar sakandare ya mayar da shi makarantar da yake jagoranta da ake kira Jama'atu 'College of Arabic and Islamic Studies' kuma a lokacin ne ya muhimmantar da harshen Larabci musamman ilmin ginin ka'idar jimla da ake cewa ilmim nahawu.

"Lallai mun yi karatu mai yawa a wannan lokacin, mun haddace mafi yawan litattafan da ake karantawa a wannan lokacin," in ji shi.

Malamin ya kuma ce yana da wani yanayi da ba ya iya barci da dare da sauki, inda a lokuta da dama mahifinsa idan ya ga ya ki tashi ya daina karatu don ya je ya kwanta sai ya kashe duka wutar gidan.

Sheik Maqary Farfesa ne da ya koyar da Larabci a Jami'ar Bayero da ke Kano amma ya ritaya a 2020.

An fara wallafa wannan hira ce ranar 5 ga watan Fabarairun shekara ta 2021.