Mutumin da ya kwashe shekaru yana ɗaukar hotunan zartar da hukuncin kisa

    • Marubuci, Swaminathan Natarajan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 8

Gargaɗi: Wannan labarin ya ƙunshi bayanai da za su iya tayar da hankalin mai karatu.

 Toshi Kazama

Asalin hoton, Toshi Kazama

Bayanan hoto, Mu'amala da fursunonin da aka yanke wa hukuncin kisa ya sauya tunanin Toshi Kazama game da hukuncin kisa

A cikin shekarun 1990, mai ɗaukan hoto haifaffen birnin Tokyo da ke Japan, Toshi Kazama yana aiki a matsayin mai ɗaukan hoto a birnin New York na Amurka, lokacin da labari game da wani matashin fursuna da aka yanke wa hukuncin kisa ya ɗauki hankalinsa.

Labarinsa ya ba shi sha'awa kuma ya yanke shawarar yana so ya gana da fursunan. Wannan shawara da ya yanke ta sauya masa yanayin aikinsa baki ɗaya.

Ya ci gaba da aiki inda ya ɗauki hoton fursunoni 22 da aka yanke musu hukuncin kisa - ɗaya a Taiwan, sauran kuma a Amurka.

Wasu daga cikinsu an aiwatar da hukuncin kisan a kansu yayin da wasu kuma ake ci gaba da tsare su a gidan yari. Ya kuma gana da ƴan'uwan ​​waɗanda abin ya shafa.

Ya ce aikinsa ya mayar da shi mai fafutukar yaƙi da hukuncin kisa.

'Yaron da babu ruwansa'

Michael Shawn Barnes

Asalin hoton, Toshi Kazama

Bayanan hoto, Kazama ya yi mamakin "kamannin mutanen kirki" na Michael Shawn Barnes, wanda aka yanke wa hukuncin kisa

Fursunan da ya fara ɗaukar hankalinsa shi ne wani matashi mai suna Michael Shawn Barnes, wanda aka yanke masa hukuncin kisa a jihar Alabama ta Amurka a shekarar 1996.

An kama shi yana ɗan shekara 17 kuma an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar zama a kujerar lantarki mai shokin bayan da aka same shi da aikata laifin kisa da kuma fyaɗe.

Kazama ya bi diddigin sa bayan ya karanta labarinsa a jarida. Bayan ya ɗaɗe ya na fama daga baya ya samu izinin kai masa ziyara a gidan yari.

Da ya gana da shi, Kazama ya ce ya yi mamaki.

"Na yi tunani, nz zata zan ga wani mugun mutum ne kawai. Amma yaron da ya bayyana a gabana yaro ne kawai wanda zan iya haɗuwa da shi a ko'ina," in ji shi.

"Na kasa jure wa buƙatar gaisawa da shi kafin na ɗauki hotonsa."

Barnes yana fama da matuƙar ƙarancin ilimi.

Lokacin da aka yanke masa hukunci, masu taya alƙali yanke hukunci sun ba da shawarar a yi masa ɗaurin rai da rai, amma alƙali ya yanke masa hukuncin kisa a maimakon haka, saboda rashin tausayin da Barnes ya nuna wa waɗanda ya aikata laifi a kansu, in ji shi.

A ranar 12 ga Yuni 1998, kotun ta sauya hukunci da aka yanke wa Barnes zuwa ɗaurin rai-da-rai.

Babu nadama?

Sean Sellers

Asalin hoton, Toshi Kazama

Bayanan hoto, An kashe Sean Sellers a Oklahoma
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sean Sellers, mutumin da Kazama ya ɗauki hotonsa a gidan yari wanda aka samu da laifin kisan kai sau uku, ya gayyace shi ya zama shaida a lokacin da aka kashe shi a Oklahoma a 1999 "a matsayin abokinsa".

Kazama ya yanke shawarar ba zai halarci kisan ba, amma ya rubuta wa Sellers wasiƙa cewa zai yi tunaninsa a lokacin da ake kashe shi.

A ranar 4 ga Fabrairu na wannan shekarar, ranar da aka shirya aiwatar da hukuncin kisan, Kazama ya kasa barci a gidansa na New York yana tunanin abin da ke faruwa a gidan yarin Oklahoma yayin da agogo ya kai 01:00.

Ya bayyana matakai daban-daban na aiwatar da hukuncin: da farko ana yi wa mutum allurar wani sinadari, sannan bayan mintuna biyar, sai a yi allura ta biyu. Na farko zai kwantar wa mutumin da hankali. Na biyu kuma ya sanya shi barci.

"Kuma na uku a 01:10 shi ne za a yi allura ta ƙarshe wadda ita ce mai kisan."

A cikin ƴan mintoci kaɗan, aka tabbatar cewa Sellers ya mutu, amma Kazama ya kasance cikin kaɗuwa ya zama kamar "matacce mai rai na tsawon watanni uku".

"Gwiwata ta yi sanyi, ban iya yin komai ba, na shiga damuwa sosai."

Kafin aiwatar da hukuncin, yayin da aka ɗaure shi a kan gadon da za a yi masa allurar kisan, an bai wa Sellers makirfo don ya yi bayaninsa na ƙarshe.

"Bai nuna nadama sosai ba, don haka dangin wanda aka kashen suka fusata."

Kazama ya yi mu'amala da fursunonin da aka yanke wa hukuncin kisa da yawa kuma ya ce gaskiya ne a ce da yawa ba sa magana kan laifukan da suka aikata.

Ya ce ya gana tare da ɗaukar hoton Napoleon Beazley, wanda aka kashe ta hanyar yin allura a shekara ta 2002 bayan samun shi da laifin kisan wani mutum mai shekaru 63 a Texas.

"Yana magana da ni game da abin da yake so ya ci kafin a kashe shi da makamantansu."

Kazama ya ce sau da yawa mutane ba sa fahimtar hakan kuma suna mamakin dalilin da ya sa wanda aka yanke wa hukuncin ba ya nuna nadama kwanaki kafin a zartar da hukuncin kisa a kansa.

An taɓa kai masa hari

Toshi Kazama

Asalin hoton, Toshi Kazama

Bayanan hoto, Kazama ya ce kasancewarsa wanda aka taɓa kai wa hari bai sanya shi ya sauya ra'ayinsa game da hukuncin kisa ba

A shekara ta 2003, Kazama yana tafiya gida tare da ƴarsa a New York lokacin da wani mutum ya kai masa hari ba zato ba tsammani inda ya kai masa duka a kai da ƙarfin gaske.

Kazama ya shaida wa BBC cewa "Ni da kaina an aikata mun laifi , an kai min hari, na yi kwana biyar a sume."

Harin ya taɓa kunnensa, inda ya zo ba ya ji sosai kuma ya samu matsalolin tsayuwa da kyau tun daga lokacin, ga kuma tabo na dindindin a kansa.

"Wannan tabon ba zai taɓa ɓacewa ba. Duk da haka, zan iya canza yadda nake kallonsa [harin]," in ji shi.

Ya yi fatan cewa maharin nasa zai ba shi hakuri, amma ba a yi nasarar gano shi ba.

Domin warwarewa daga wannan kaɗuwar, ya ce mutane irin su Bud Welch ne suka zaburar da shi wanda ƴarsa Julie Marie mai shekaru 23, tana cikin mutane 167 da aka kashe a harin bam da aka kai kan ginin gwamnatin tarayya a birnin Oklahoma a shekarar 1995.

Da farko Mista Welch ya fusata bayan rasa ƴarsa kuma yana goyon bayan hukuncin kisa, amma daga baya ya fara fafutukar ganin an soke shi.

Kazama na da ra'ayin cewa hukuncin kisa ba ya taimaka wa iyalan wadanda abin ya shafa su jure da asararsu. Yana son a bai wa iyalai wani tallafi na daban, gami da kuɗi.

"Iyalan wanda abin ya shafa ne suka fi shan wahala. Amma jama'a sukan yi kuskure kuma suna tunanin ni ne wanda aka zalunta kuma [don haka] zan [so] ɗaukar fansa.

"Wannan gurabtaccen tunani ne da mu ke da shi."

Kazama ya ce wannan tunani na ƙarfafa goyon bayan aiwatar da hukuncin kisa.

'Mataki ɗaya kacal'

Irvin Harris

Asalin hoton, Toshi Kazama

Bayanan hoto, Kazama yana tattaunawa da Irvin Harris, wanda aka yanke masa hukuncin kisa sau biyu amma aka sake shi bayan shekaru 23, a gidan yarin Louisiana.

Mafi girman karamcin da aikin Kazama ya taɓa samu ya zo ne a shekara ta 2005 lokacin da Kotun ƙoli ta Amurka ta yi amfani da hotunansa a matsayin shaida a shari'ar Roper Simmons inda aka yanke hukuncin cewa ya saɓa wa kundin tsarin mulkin kasa idan aka zartar da hukunci kisa a kan wanda bai kai shekara 18 da haihuwa ba a lokacin da ya aikta laifin.

"Na yi farin ciki cewa hotunan sun yi tasiri mai kyau," in ji shi.

"Har yanzu da sauran abubuwa da dama da suka rage in yi," in ji Kazama. "Wannan mataki ɗaya ne kacal. Na an samu kwanciyar hankali kaɗan (a lokacin da aka yanke hukuncin). Ba na jin kamar nasara ce."

Kazama

Asalin hoton, Toshi Kazama

Bayanan hoto, Kazama ya kaɗu sosai lokacin da ya gano yadda kujerar lantarki mai shokin ke aiki

Mu'amalarsa da masu gadin gidan yari ta sa ya gane cewa yin aiki da fursunonin da aka yanke wa hukuncin kisa yana da matuƙar tasiri a kansu.

A ziyararsa ta farko zuwa gidan yarin Alabama, ya ga masu gadi suna shirya aiwatar da hukunci kisa a kan wasu masu laifi.

"Lokacin da na shiga zauren da ake aiwatar da hukuncin kisan, ina jin kamshin naman mutane da ya ƙone," kamar yadda ya shaida wa BBC.

A kusa da zauren akwai wurin da ake tsare da waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa. Kazama ya ce bai manta yadda fuskar fursunan da ya haɗu da shi a wurin ba.

"Masu gadi sun ce matattace ne da ke tafiya."

Sun kuma shaida masa yadda suke aikin tattara gawar mutumin bayan an kashe shi.

Bayan ziyararsa ta farko, ya ci gaba da ɗaukar hoton fursunonin da aka yanke musu hukunci a wasu gidajen yari, kuma ya ce jami'ai sukan faɗa masa irin wannan labarin.

"Toshi don Allah ka gaya wa duk duniya kar mu daina kashe mutane."

A gidajen yarin Amurka, kujerun lantarki masu shokin suna da maɓallan kunnawa biyu ko uku, ta yadda ba a sanya wani mai zartar da hukuncin kisa guda ɗaya ya ji alhakin mutuwar mai laifin.

Ƙasar Japan tana aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya, kuma gidajen yarin akwai makullai guda uku don buɗe kofar tarkon da wanda aka yanke wa hukuncin ya rataya a sama, amma ɗaya ne kawai ke aiki don haka masu gadin ba su san wanda zai buɗe ba, in ji shi.

Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta ce a shekarar 2024 an zartar da hukuncin kisa 1,518, a duniya.

Inda Iran da Iraki da Saudiya ke da jimillar mutane 1,380, yayin da Amurka ke da 25.

Amnesty ta ce alƙaluman ba su haɗa da dubban mutanen da ake tunanin an kashe a China ba saboda ƙasar ba ta fitar da alƙaluman adadin hukuncin kisa da take aiwatarwa duk shekara.

Gwagwarmaya na gaba

Christa Pike

Asalin hoton, Toshi Kazama

Bayanan hoto, Hukumomi a Tennessee sun sanya ranar 30 ga Satumba 2026 a matsayin ranar da za a aiwatar da hukuncin kisa kan Christa Pike.

Ɗaya daga cikin fursunonin da Kazama ya gana da ita, ita ce Christa Pike, wadda aka samu da laifin kashe wata matashiya ƴar shekara 19 mai suna Colleen Slemmer, a lokacin tana da shekaru 18 kacal a shekarar 1995.

Hukumomi a Tennessee sun sanya ranar 30 ga Satumba 2026 a matsayin ranar da za a aiwatar mata da hukuncin kisa.

Idan har aka aiwatar da shi, zai kasance karo na farko da aka yanke wa wata mace hukuncin kisa cikin fiye da shekaru 200 a jihar.

Lokacin da ya same ta, Kazama ya ce "ta kasance kamar yarinya mai hankali, na kasa yarda cewa za ta iya aikata irin wannan aikin. Ta ce ta yi".

Pike ba ta nuna nadama ba, in ji shi.

Kazama bai yi magana da Pike na tsawon shekaru ba, amma labarin kisan da aka shirya aiwatarwa a kanta ya sanya shi tunani mai zurfi game da ita.

Ya ce yana son ko ta yaya ya yi ƙoƙarin ganin an dakatar da hukuncin kisa a kanta: "Dole ne in yi magana da lauyan da ke kare ta a halin yanzu game da matakin da ya dace don kuɓutar da ita daga kisa."