An soke wasannin Serie A a Italiya sanadiyyar rasuwar fafaroma

...

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Fafaroma Francis ya rasu ne bayan fama da cutar sanyin ƙashi mai tsanani
Lokacin karatu: Minti 1

An dakatar da wasanni guda huɗu na gasar Serie A ta ƙasari Italiya bisa rasuwar Fafaroma Francis.

A ranar Litinin fadar Vatican ta sanar da rasuwar fafaroman wanda ya shafe shekara 88 a duniya bayan wata jinya da ya yi har aka kwantar da shi a asibiti.

Karawar da aka soke ta haɗa da: Torino v Udinese, Cagliari v Fiorentina, Genoa v Lazio and Parma v Juventus.

Hukumar da ke lura da gasar ta Serie A a ƙasar ta ce za ta duba wani lokacin da za a buga wasannin a nan gaba.

Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da dama sun miƙa ta'aziyyar su bisa rasuwar shugaban cocin katolikan na duniya.