Farfesan da ke sana'ar walda a Najeriya
Farfesa Kabir Ahmed da ake yi wa laƙabi da Abu Bilal ya bambanta da sauran farfesoshi a Najeriya, waɗanda ke dogara kawai da sana'ar koyarwa a jami'o'i, shi a nasa ɓangare yana gudanar da sana'ar walda a matsayin sana'a ta biyu a garin Zariya da ke arewacin ƙasar.
Ana ƙallon sana'ar walda a matsayin ƙaramar sana'a musamman a Najeriya, lamarin da ya sa labarinsa ya bai wa mutane da dama mamaki, musamman abokan sana'arsa, bayan ya buɗe warin gudanar da sana'ar.
"Bana jin wata shakkar kasancewata mai walda duk da cewa ni farfesa ne, saboda ina samun kuɗi ta hanyar sana'ar,'' kamar yadda ya bayyana wa BBC.
Malamin jami'ar mai shekara 50 - wanda ke duba ɗaliban da ke bincike a tsangayar koyar da injiniyanci a jami'ar Ahmadu Bello da Zariya, ɗaya daga cikin manyan jami'o'i a ƙasar - ya kwashe shekara 18 yana koyarwa tare da wallafe-wallafen littafai.
Ɗaya daga cikin takwarorinsa malaman jami'a, Farfesa Yusuf Jubril, ya bayyana yadda abokin aikin nasa ya zo da baƙon al'amari wa mutane.
''Al'umma sukan mu yin tunanin cewa mun girmi gudanar da wasu sana'o'i, kuma ba haka batujn yake ba'', in ji shi.
"Abin da yake yi ba kaskanci ba ne, abu ne da ya kamata a yaba masa, kuma ina fatan saura za su yi koyi daga gare shi."

Abu Bilal ya ce yana da kyau mutane, musamman waɗanda suka kammala karatu, su riƙa faɗaɗa tunaninsu kan yadda za su samu abin dogaro da kawunansu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Ilimi ba zai hana ka gudanar da irin waɗannan sana'o'i ba, na yi mamakin yadda mutane musamman waɗanda ke da digiri na farko ke kallon irin waɗannan sana'o'i a matsayin ƙanƙanci.''
Kalamansu sun yi daidai da wani rahoto da ya ce fiye da kashi 40 na waɗanda ke kammala jami'a ba sa samun aikin gwamnati a Najeriya, ƙasar da ta fi kowace yawan al'umma a nahiyar Afirka.
Malamin ya buɗe wani ƙaramin wajen walda a Zariya kusan shekara 20 da suka gabata.
A shekarar 2022, shekara guda bayan ya zama farfesa, ya koma wani sabon wur mai girma, inda ya buɗe sana'o'i masu yawa a garin.
hakan ya ba shi damar sayo ƙarin kayan aiki masu yawa, tare da gudanar da manyan ayyuka, inda kwastomominsa ke zuwa don yi musu abubuwa kamar ƙofar ƙarfe da tagogi da sauran abubuwa.
"Nakan yi sana'a komai ƙanƙantarta, ko da ƙofa guda ce nakan yi mata walda cikin jin daɗi domin a biyani,'' in ji shi.
Tun yana matashi, Farfesan ya ce yake ta sha'arwar gyaran abubuwa irinsu radiyo, lamarin da ya kai shi ga karatun fanin injiniya.
"Sai dai abin mamakin, sai na fahimci injiniyanci da ake koyarwa a jami'a a takarda ne kawai, don haka ina buƙatar wurin da yi riƙa aiwatar da shi a aikace,"in ji shi
"Wannan sha'arwa ce ta sa na buɗe shago don fara walda''.
Ba wai don cika burinsa ne kawai ya buɗe shagon ba, sana'ar na taimaka masa wajen samun abin biyan buƙatunsa na yau da kullum.
Malaman jami'a a Najeriya sun daɗe sun fafutikar samun albashi mai gwaɓi, inda da yawansu ke samun albashin naira 350,000 zuwa 500,000 a wata, inda suka jima suna gardama da gwamnati kan ƙarin albashin.
Farfesa Abu Bilal ya ce sana'arsa ta walda na ba shi damar samun abin biyan buƙatunsa, lamarin da ya sa har ya samu damar sayen ƙaramar motarsa mai kyau kirar 'Mercedes'.
"A lokacin da malaman jami'a muka tsunduma yajin aiki na kusan wata takwas a shekarar 2022, kuma gwamnati ta daina biyanmu albashi, ban rasa abin kashewa ba saboda wannan sana'ar, kuma wasu daga cikin takwarorina kan o wajen domin in taimaka musu''.
Farfesa Abu Bilal na fatan janra'ayin sauran mutane irinsa da su rungumi sana'o'i irin nasa.

Yana da yara 10 a shagon masu shekaru tsakanin 12 zuwa 20, da ke samun kwarewa kan sana'ar a wajen shehin malamin jami'ar.
Waɗanda ba su je makaranta da rana ba, ke kula da shagon da rana idan malamin yana jami'ar.
Masu koyon sana'ar kan yi shekara guda a shagon Farfesan - sannan su je su buɗe nasu wuraren sana'ar bayan ya yayesu
"Na koyi abubuwa da dama a wurin, a yanzu ina iya yin abubuwa masu yawa ta hanyar walda,'' in ji wani matashi mais hekara 18 da ke koyon sana'ar a wurin.
"Duk da cewa mu masu koyon sana'a ne, yana ba mu naira 10,000 a kowane wata, baya ga kuɗin abinci da yake ba mu a kowacce rana''.
Shehin malamin jami'ar ya kuma ce yana fatan 'ya'yansa biyar su koyi sana'r tasa domin dagora da kawunansu.
''Nakan zo da su wajen sana'ar a ranakun da babu makaranta domin su ga yadda ake gudanar da wannan sana'ar, ina so su koyi sana'ar saboda wata rana''.
A ganin Farfesa Abu Bilal wannna sana'ar tasa ba za ta hana shi sauke nau'in koyarwa da yake yi a jami'a ba, saboda shi ma aikin koyarwa aiki ne da yake da sha'awarsa sosai ''Ina son koyar da ilimi.''












