Lafiya Zinariya: Dalilan da ke sawa a juyar da mahaifar mace

Lafiya Zinariya: Dalilan da ke sawa a juyar da mahaifar mace

Matsalolin kiwon lafiya da suka haɗa da fashewar mahaifa na daga cikin manyan dalilan da ke sanya wa a juyar da mahaifar mace.

A cewar likitoci ana yi wa mace aiki ne a asibiti idan za a juyar da mahaifarta. Haka kuma ba a yin tiyatar sai da yardarta da na miji ko makusantanta.

Matar da aka yi wa juyen mahaifa bata sake haihuwa, idan kuma bata taɓa haihuwa ba, hakan na nufin ba zata haihu ba.

Likitoci sun bayyana cewa tiyatar tana sa a raba bututun hannun mahaifa da jakar ƙwan mace, kuma hakan na hana ƙwai ya haɗu da maniyyin namiji da zai kai a samu ɗa.

Raba bututun hannun mahaifar ko ɗaureta ana yinsa ne da niyyar ba za a sake kwancewa ba.

Wannan hanya ta kasance babbar hanyar dakatar da haihuwa da mata ke bi a faɗin duniya.

Latsa makunnin da ke sama, don ji daga bakin wata ƙwararriyar likitar mata a Najeriya, Farfesa Yamuna Aminu Ƙani.

Ta yi ƙarin bayani kan wannan batu da ma matsalolin da kan iya biyo baya, idan ta kama an gyara ko kwance ɗaurin da aka yi wa bututun hannun mahaifar.