Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tauhidi ne a cikin wakar Dawo-Dawo - Naziru Sarkin Waka
Latsa hoton da ke sama domin kallon hira da Naziru Sarkin Waka:
Fitaccen mawakin nan na Hausa, Naziru M. Ahmad wanda aka fi sani da Naziru Sarkin Waka ya ce yana matukar kaunar wakarsa ta Dawo-Dawo Labarina saboda tauhidin da ya saka a cikinta.
Ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da BBC Hausa.
Ya ce: "Nan kusa yanzu ban da wakar da nake ji da ita saboda nasarar da na samu wajen jefa wannan tauhidin ya shiga ciki, irin wannan wakar gaskiya," in ji shi.
Wakar, wadda ya zuwa yanzu mutum fiye da miliyan daya da dubu dari bakwai suka kalla, tana cikin wakokin da aka sanya a shahararren shirin nan na shirin Labarina Series.
Ya kara da cewa wakar "ba wani shirri take da shi ba illa waka ce ta fim din Labarina."