NIMC: Abin da ya kamata ku sani kan lambar dan kasa ta NIN a Najeriya

Ku latsa hoton da ke sama domin sauraron bayanin hukumar NIMC

A Najeriya, jama'a na ta ribibin ganin sun sada lambobin wayarsu ta salula da lambar shaidar dan kasa kamar yadda gwamnati ta bayar da umarni.

Hukumomin kasar dai sun sanar da bullo da wata sabuwar manhajar wayar salula da mutane za su iya saukewa daga shagunan Play Store ko App Store domin ba su damar haɗa lambar wayarsu ta salula da lambar shaidar zama dan kasar da ake kira National Identification Number (NIN).

Wannan na faruwa ne yayin da a bangare guda jama'a ke ci gaba da kokawa kan cunkoso da jinkiri a cibiyoyin yin rajista domin samun lambar.

Hadiza Dagabana, darakta ce a Hukumar Shaidar Dan Kasa ta Najeriya wato NIMC, ta yi wa Ishaq Khalid karin bayani kan sabuwar manhajar mai suna NIMC Mobile App.