'Dalilan gwamnatoci na ɓoye kayan tallafi ihu ne bayan hari' - Comrade Kabiru Sa'idu Dakata
Ku latsa lasifikar da ke sama don sauraron cikakkiyar hirar:
A Najeriya, hukumomi a jihar Filato sun ce sun kama mutum sama da 200 bisa zarginsu da hannu wajen aukawa suto suton gwamnati su ka wawashe abinci.
Ba a jihar Filato ba kadai, lamarin ya faru a wasu jihohin Adamawa da Kaduna da Taraba da Abuja da Cross River da kuma Kwara.
A jihohin ƙasar da dama al'umma sun wayi garin Litinin cikin dokar hana fita da hukumomi suka ƙaƙaba ta tsawon sa'a 24, bayan zanga-zangar nuna adawa da rundunar 'yan sanda SARS ta rikiɗe zuwa tarzoma.
Kan wannan batu BBC ta tattauna da Comrade Kabiru Sa'idu Dakata, babban daraktan Cibiyar wayar da kan al'umma kan shugabanci na gari da tabbatar da adalci (CAJA).