Matashiyar da ke zane don karfafawa mata gwiwa

Ranar 15 ga watan Yuni na kowacce shekara majalisar dinkin duniya ta ware don yaba wa matasa da ke amfani da hazakar da Allah ya yi musu wajen inganta rayuwar al'umma.

Mun tattauna da Hafsat Sani Sami, yar shekara 28 mai yin zane don karfawawa mata gwiwa.

Ban da haka, tana rina yaduka da hada 'yan kunne. Baiwa ce ta ce take da ita tun tana karamar yarinya.