BBC Africa Eye: An bankaɗo masu sayar da magungunan bogi na COVID-19 a Ghana

Bayanan bidiyo, BBC Africa Eye ta gudanar da bincike kan likitocin bogi da magungunan korona na bogi.

A yayin da cutar korona take ci gaba da addabar duniya, shirin BBC Africa Eye ya bankado yadda wasu likitocin bogi da 'yan damfara suke samun kudade masu dimbin yawa ta hanyar sayar da magungunan cutar na jabu.

Dan jaridar nan mai binciken kwakwaf Anas Aremeyaw Anas ya yi ɓad-da-kama a Ghana, inda ya fallasa masu sayar da magungunan Covid-19 na bogi suna karbar dubban daloli.