"Duk da kashe Ahmed Suale ba za mu bar binciken kwakwaf ba” - Anas Aremeyaw Anas
Sashen Hausa na BBC ya samu tattaunawa da dan jarida mai binciken kwakwaf na kasar Ghana, Anas Aremeyaw Anas.
Dan jaridan shahararren ne a fannin aikin jarida na binciken kwakwaf ta hanyar daukar hoto ko bidiyo na masu aikata laifin cin hanci da rashawa a lokacin da suke yi.
Daga cikin bincikensa akwai; "Doctor Dra", na wani likitan da ke zubar wa da mata ciki amma yana kwana da su a kafin ya yi masu tiyata.
Bincikensa ya jawo kora da daure jami'an kasashe daban-daban a kan laifin aikata rashawa.

Asalin hoton, Anas Aremeyaw Anas
A farkon shekarar 2019 ne aka harbe kashe abokin aikinsa Ahmed Hussain Suale ta hanyar harbinsa da bindiga.
A cewar Anas, "Ni da Ahmed Suale daman akwai wadanda suke neman mu su kashe mu, amma sai muka tsallake"
"Amma duk abin da Allah ya kaddarawa mutum ko da zai je sama ko kasa sai ya same shi" a cewar Anas din.

Asalin hoton, Anas Aremeyaw Anas
Ya kuma sha alwashin cewa ba za su bari mutuwar Ahmed ta hana su binciken kwakwaf ba.

Asalin hoton, Anas Aremeyaw Anas
"Su masu aikata abubuwan nan marassa kyau, burinsu shi ne idan suke kashe Ahmed sai mu bar aikin, amma ba za mu bari ba"
Ya kara da cewa "Ahmed dake a wajen Allah idan ya ga kamar mun bar aikin nan abin ba zai masa dadi ba"

Asalin hoton, Anas Aremeyaw Anas
Anas kuma ya shaida mana cewa akwai wani aikin da suke yi a Najeriya mai suna 'Nigeria Investigates' domin su yi yaki da rashawa.
Ya bayyana cewa zai ci gaba da kulle fuskarsa domin su na yin hakan ne saboda tsaron rayukansu.

Asalin hoton, Anas Aremeyaw Anas
Cikakkiyar hirara na a shafinmu na Youtube, www.youtube.com/user/bbchausa