Ba na goyon bayan hana Almajirci - Rochas Okorocha

Bayanan bidiyo, Ba na goyon baya hana Almajirci - Rochas Okorocha

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Tsohon gwamnan jihar Imo kuma Sanata a yanzu Rochas Okorocha, ya soki gwamnonin arewa kan hana almajirci.

Sanatan ya nemi a inganta almajirci inda ya yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni da su taimaka wa tsarin.

Rochas ya ce "mafi yawancin manyan da ke gare mu a yanzu sun yi almajirci."

Okorocha ya ce gidauniyarsa na da makarantu a Kano da Zariya da Yola da Sakkwato, kuma duka almajirai yake taimaka wa domin su samu ilimi.

An daɗe ana ce-ce-ku-ce kan batun almajirci a Najeriya musamman illolinsa da kuma makomar yaran da ake tura wa almajiranci.

Bidiyo: Abdulbaki Jari