Buhari ya sa baki kan batun Zainab Aliyu

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci Ministan Shari'a Abubakar Malami da ya shiga maganar Zainab Aliyu, 'yar Najeriyar nan da ke tsare a kasar Saudiyya.
Jami'an tsaron Saudiyya sun kama Zainab Aliyu ne jim kadan bayan sun isa Saudiyya don yin aikin Umara ita da mahaifiyarta Maryam da kuma 'yar uwarta Hajara.
Sun zarge ta da safarar kwayar Tramadol har guda 2,000 bayan da aka ga kwayoyin a wata jaka mai dauke da sunanta.
Amma tuni hukumar yaki da ta'ammali da miyagun kwayoyi ta NDLEA ta bayyana cewa wasu ma'aikata ne a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano (MAKIA) suka saka mata kwayar a jakarta.
Kwamandan hukumar mai kula da MAKIA Ambrose Omorou ya tabbatar wa da BBC cewa tuni suka kama mutum shida, wadanda ake zargi da aikata hakan.

Uku daga cikinsu ma'aikata ne da ke tantance kayayyakin matafiya, daya ma'aikacin wani kamfanin sufurin jirgin sama ne, sauran biyun kuma jmai'an tsaro ne a filin jirgin saman.
Kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter, Abike Dabiri-Erewa mataimakiya ta musamman ga Shugaba Buhari kan harkokin kasashen waje ta ce shugaban ya umarci Abubakar Malami da ya shiga maganar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
"Buhari ya umarci ministan shari'a da ya yi dukkanin mai yiwuwa don ganin an yi wa Zainab adalci. Mahaifinta ne ya sanar da mu kuma muna samun ci gaba game da ita da sauran mutum biyun," kamar yadda Abike Dabiri ta bayyana.
Wannan ya biyo bayan maganar da Sanata Shehu Sani ya yi ne, inda yake shawartar iyayen Zainab da su kawo kokensu gaban majalisar dokokin kasar domin ta shiga lamarin.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Dabiri ta kuma shaida wa jaridar Premium Times cewa Buhari ya shiga lamarin a lokacin da ya samu labari mako biyu da suka gabata.
Me 'yan Najeriya ke cewa?
'Yan Najeriya da dama ne a 'yan kwanakin nan suka cika shafukan sada zumunta da kiraye-kiraye ga hukumomi da a yi wa Zainab adalci.
Sun yi amfani da maudu'ai kamar #FreeZainab #JusticeForZainab a shafin Twitter.
Hukumar kare hakki ta Amnesty International ma ta yi irin wannan kira.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3

Karshen labarin da aka sa a X, 4
Wasu dalibai da suka yi ikirarin abokan karatunta ne a jami'ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano sun ce za su gudanar da zanga-zangar lumana ta nemar wa Zainab adalci.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 5