Ana ce-ce-ku-ce kan haramta hakar zinari a Zamfara
Latsa lasifika a hoton sama domin sauraren ra'ayoyin 'yan Zamfara
Ra'ayi ya bambanta tsakanin al'ummar jihar zamfara kan matakin gwamnatin Tarayya na haramta hako ma'adinai a jihar da nufin tabbatar da tsaro.
Sufeto janar na 'yan sandan Najerya ne ya sanar da daukar matakin tare da umurtar 'yan kasashen waje da ke aikin hako ma'adinan su fice daga kasar.
Wannan na zuwa bayan zanga-zangar da 'yan Najeriya suka kaddamar a Abuja da wasu sassan kasar kan yawan kashe-kashe a Zamfara, inda suka yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi wani abu cikin gaggawa.
Wasu 'yan Zamfara sun bayyana ra'ayoyinsu kan matakin haramta hako ma'adinai a jihar da nufin magance matsalar tsaro.