Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko za a iya rayuwa har abada?
Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Shin za mu iya amfani da kimiya don mu rayu har abada?
Yawancin masana kimiya suna son sanin yadda halittar mutane za ta sauya nan gaba, amma inganta halittarmu don mu rayu har abada ka iya kasancewa abu da ya fi kusa fiye da yadda muke tsammani.
Sauya halittar dan adam wata tafiya ce wadda ke son amfani da fasaha da kuma fikirar na'ura domin sarrafa yadda makomar halittarmu za ta kasance, a cewar masana kimiyar.