Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Obasanjo bai isa ya hana ni komai ba - Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya ce tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo ba ya taba yaba abin da wani ya yi.
Alhaji Atiku yana mayar da martani ne kan tambayar da Jimeh Saleh na BBC ya yi ma sa dangane da kalaman Obasanjo, inda ya ce ba zai taba barin Atiku ya yi shugabancin Najeriya ba matukar yana raye.