Rayuwar kwallon Cristiano Ronaldo cikin hotuna

Bayan da Cristiano Ronaldo ya kammala komawa Juventus a kan fam miliyan £99.2 daga Real Madrid inda ya zura kwallo 451 a wasa 438, mun yi nazari kan rawar da ya taka cikin hotuna.

Ronaldo a Sporting Lisbon

Asalin hoton, Science Photo Library

Bayanan hoto, Matashi Cristiano ya fara taka-leda ne a kulob din Sporting Lisbon na Portugal a matsayin dan wasan gefe mai gudu. Rawar da ya taka a wasansu da Manchester United ce ta sa Sir Alex Ferguson ya sayo shi nan take.
Ronaldo playing for Manchester united

Asalin hoton, Manchester United

Bayanan hoto, Farkon zuwan Manchester United, an yi hasashen cewa zai zamo dan wasan mai lango, wanda zai rinka saurin faduwa idan aka kusance shi. Amma nan take sai ya daura damara abin da ya bashi damar lashe kofin Firimiya uku, FA daya da kuma zakarun Turai daya a 2008.
Ronaldo yana murza-leda a Real Madrid

Asalin hoton, YOSHIKAZU TSUNO

Bayanan hoto, Ya zamo dan wasan da ya fi kowa tsada a duniya lokacin da ya koma Real Madrid a 2009. Ya taka muhimmiyar rawa a can inda ya zamo gawurtaccen dan kwallo. Ya lashe kofin zakarun Turai hudu sannan ya zamo wanda ya fi kowa cin kwallo a kulob din. Amma ya sha nuna alamun rashin jin dadi a can din tare da yin barazanar barin kulob din a lokuta da dama.
Ronaldo da lambar yabo ta Ballon d'Or

Asalin hoton, Power Sport Images

Bayanan hoto, Amma hakan bai shafi kokarinsa a filin wasa ba. Ya lashe kyautar Ballon d'Or ta dan kwallon da ya fi kowanne a duniya sau biyar!
Ronaldo holding european championship trophy

Asalin hoton, ullstein bild

Bayanan hoto, Ya kuma taka rawa a matakin kasa da kasa. Duk da cewa an fitar da Portugal da wuri daga gasar kofin duniya ta Rasha 2018, Ronaldo ya jagoranci kasarsa ta lashe gasar kofin kasashen Turai ta 2016 duk da ya samu rauni a wasan karshe.
Ronaldo dauke da kofin zakarun Turai

Asalin hoton, VI-Images

Bayanan hoto, Ronaldo ne dan kwallo daya tilo da ya lashe kofin zakarun Turai sau biyar kuma Juventus za ta yi fatan ya taho da wannan nasarar ta sa zuwa kulob din.