Kalli yadda ake zabe a Kenya

Ana sake zabe shugaban kasa a Kenya ne bayan kotu ta ce an tafka kura-kurai a zaben farko da aka gudanar a watan Agusta-Ga yadda zaben ke gudana.

Kenya
Bayanan hoto, Wasu sun fara kada kuri'unsu yayin da wasu ke kan layi
Kenyan Ellection
Bayanan hoto, Wani wakilin BBC ya ce da alamu mutane ba su fito zaben ba sosai kamar yadda suka fito zaben da aka yi a watan Agusta
Garissa
Bayanan hoto, Yayin da masu zabe suke layi a wurare irin su karamar hukumar Kiambu, rahotanni daga garin Garissa na cewa an kaurace wa rumfunan zabe ne
Kenyan Ellection

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Su kuma masu zanga-zanga a unguwar marasa galihu ta Kibera sun yi fama da hayaki mai sa hawaye da 'yan sanda suna harba
Kenyan Ellection

Asalin hoton, Citezen TV

Bayanan hoto, Yayin da Shugaba Uhuru Kenyatta ya kada kuri'arsa, shi kuma madugun 'yan adawa, Raila Odinga kaurace wa zaben ya yi
Kenyan Ellection
Bayanan hoto, Duk da cewa ana ganin fitowar masu zabe domin kada kuri'a bai kai na watan Agusta ba, mutane daga mataki daban-daban sun fito zaben
Kenyan Ellection

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Jami'an tsaro sun yi ta arangama da masu zanga-zanga
Kenyan Ellection

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Baya ga harbi, jami'an tsaro sun amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma ruwan zafin wajen tarwatsa masu zanga-zanga
Kenyan Ellection

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A halin yanzu dai babu tabbacin yadda zaben da jagoran 'yan adawa Raila Odinga ya kauracewa zai kasance