Gane Mini Hanya: Hira da gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule
Danna hoton sama domin sauraren hirar
Gwamnan jihar Nasara Abdullahi Alhaji Sule ya ce kammala ayyukan da ya fara su ne mafi muhimmanci a gabansa fiye da neman wa’adi na biyu na mulkin jihar.
Gwamna Abdullahi Sule ya ce ba ya cikin gwamnonin Najeriya da suka damu da sake samun dama karo na biyu don su kammala wasu ayyuka.
A wannan hira ta musamman da abokin aikinmu Yusuf Ibrahim Yakasai, gwamna A A sule ya bayyana matsayarsa kan zaben da aka yi wa Sanata Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam’iyyar APC.
Amma Yusuf ya fara da tambayarsa kan alkawarin da ya yi gabanin zaben 2019 kan cewa zai nemo masu zuba jari da za su samar da ayyukan yi ga matasan jihar ta Nasarawa.