Lafiya Zinariya: Abubuwan da suka kamata a yi wa jariri mai yawan kukan dare

Bayanan sautiLafiya Zinariya: Abubuwan da ake yi wa jariri mai kukan dare

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Masana a fannin kiwon lafiya sun ce jarirai masu kukan dare sukan fara ne tun daga makonni biyu da haihuwa zuwa mako shida wasu kuma har fiye da hakan.

Jariran na yin kukan ne ba tare da wani dalili na zahiri da ke sanya su kukan ba. In ji hukumar lafiya ta Burtaniya.

Inda ta kara da cewa a kimiyance babu wani dalili da ke janyo wannan kuka, duk kuwa da cewa a al'adance mutane na danganta shi da dalilai da dama.

Haka kuma a mafiya yawancin lokuta su kan fara kukan ne daga maraice zuwa cikin dare.

Shafin intanet na hukumar ya kuma bayyana cewa, ana gane kukan dare ne idan jariri yana kuka fiye da sa'oi uku a rana kuma ya kwashe kimanin kwana uku yana hakan, a cikin mako guda.

Haka zalika NHS ta ce kula da jaririn da ke cikin wannan yanayi yana da tayar da hankali da kuma gajiyarwa.

Amma ta bayar da shawarar mace ta nemi taimakon 'yan uwa ko kawaye ko ma abokan arziki.

Kukan sabon jaririn da a turancin ingilishi a ke cewa Colic, jariri na daina kukan idan ya kai tsawon makonnin da aka ambata tun daga farko ba tare da an bashi wani magani ba.

Sai dai hukumar ta ce akwai wasu dabaru da uwa za ta iya yi don samun saukin kukan.

Wadanda suka hada da rungume shi ko dora shi a kafada tana jijjiga shi ko ta yi masa wank da ruwan dumi.

Wani abu mai muhimmanci kuma shi ne uwa ta tsayar da jariri ta shafa bayansa da zarar ya gama cin abinci har sai ya yi gyatsa. In ji hukumar.

To domin jin wasu karin abubuwan da za ku iya yi wa jariri mai kukan dare sai ku saurari hirar Habiba Adamu da wata kwararriyar likitar yara, Dr. Naja'atu Hamza