Lafiya Zinariya: Jinin haila a tsakanin 'yan mata
Latsa hoton da ke sama don jin cikakken shirin
Samun ilimi game da haila na da muhimmanci ga duk 'ya mace tun kafin ta fara jinin na al'ada.
Haka kuma tsafta na da muhimmancin gaske ga macen da take jinin al'ada, duk kuwa da cewa mata da dama ne basa samun zarafin sayen audugar mata don amfani da ita a duk wata.
Wannan matsalar ta shafi 'yan mata 'yan makaranta a sassa daban-daban na duniya.